Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Nkurunziza

Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Nkurunziza

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa bisa rasuwar Shugaba Pierre Nkurunziza na kasar Burundi.

Ya ce Nkurunziza mutum ne mai kishin kasa da ya yi wa kasarsa jagoranci a mawuyacin lokaci da hikima da hangen nesa.

Idan ba a manta ba dai Shugaba Nkurunziza ya rasu ne a ranar Litinin sakamakon buguwar zuciya.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 55 a duniya.

Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Nkurunziza
Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Nkurunziza. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A sakon ta'aziyar da babban hadiminsa a kan watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar ranar Talata a Abuja, Shugaban Najeriyan ya jajintawa iyalai, gwamnati da mutanen Burundi.

Ya ce, "Na yi matukar bakin cikin samun labarin rasuwar Shugaba Pierre Nkurunziza.

"Shugaba Nkurunziza mutum mai mai kishin kasa da ya yi wa kasarsa jagoranci a mawuyacin lokaci da hikima da hangen nesa.

"A wannan lokacin na bakin ciki, gwamnati da mutanen Najeriya da ni kai na muna mika sakon ta'aziyar mu ga gwamnati da mutanen Burundi.

"Muna ta'aziya tare da addua ga iyalan Shugaban kasar.

"Da fatan Allah ya basu ikon jure wannan rashin."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel