Dokar cin-gashin-kan Majalisar jihohi da bangaren shari’a: Babu gudu babu ja da baya - Buhari

Dokar cin-gashin-kan Majalisar jihohi da bangaren shari’a: Babu gudu babu ja da baya - Buhari

- Bayan an kai ruwa rana, gwamnoni 36 na kasar nan sun karbi dokar cin gashin kan majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi a matsayin kaddara

- Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da sauran takwarorinsa sun rungumi kaddara bayan da fadar shugaban kasa ta ce babu gudu babu ja da baya a kan sabuwar dokar

Gwamnati a Najeriya ta bayyana cewa, babu gudu babu ja da baya a kan fara aiki da sabuwar dokar cin gashin kan majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi.

A ranar Talata, 9 ga watan Yuni, gwamnatin Tarayya ta ce sabuwar dokar mai suna 'Executive Order 0010', da shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar ta na nan daram.

Lauyan Koli kuma Ministan Shari'a na Najeriya, Mallam Abubakar Malami (SAN), shi ne ya fayyace hakan kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Buhari da Ministan Shari'a; Abubakar Malami (SAN)
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Buhari da Ministan Shari'a; Abubakar Malami (SAN) Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Sai dai a madadin haka, Ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta yi aiki tare da Gwamnonin Jihohi domin shimfida hanyoyin aiwatar da dokar cikin tsari mai hadi da inganci.

Ya ce kwamitin aiwatar da dokar zai gabatar da tsare-tsare masu muhimmanci ga Kungiyar Gwamnonin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki.

KARANTA KUMA: Namibia ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka tituna masu kyau - Africa Facts Zone

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta yaba da yadda gwamnonin suka amince da yin amfani da kundin tsarin mulkin ƙasa wajen bai wa majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi 'yanci.

A yayin da a yanzu gwamnoni suka karbi wannan sabuwar doka hannu biyu, Ministan ya ce za ta kara kyautata tsarin dimokuraɗiyya a fadin kasar tun daga tushe.

Malami ya fayyace cikin wata sanarwa a birnin Abuja ta hannun Mataimakin sa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Dr. Umar Jibrilu Gwandu.

Wannan karin haske ya zo ne sabanin rahotannin da ake yadawa na cewa shugaban kasa ya dakatar da fara aiki da dokar cin gashin kan majalisun dokoki da bangaren shari'a.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

An ruwaito cewa, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce shugaba Buhari ya dakatar da fara aiki da sabuwar dokar ne saboda rashin jin dadi da gwamnonin suka nuna.

Gwamnonin sun nuna damuwa kan dokar da za ta ba wa majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi damar samun kudadensu kai-tsaye ba tare da ya bi ta hannun gwamnoni ba.

A karkashin wannan sabuwar doka, Buhari ya ba wa Ofishin Akanta Janar na kasa umarnin cire wa majalisun dokoki da bangaren shari’a kudaden su daga asusun duk wata jiha da ta ki bin wannan umarni.

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2020, shugaban Najeriya ya rattaba hannu a kan dokar da ta ba majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi 'yanci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel