'Yan Boko Haram sun kashe mutum 69 a wani kauye a Borno

'Yan Boko Haram sun kashe mutum 69 a wani kauye a Borno

'Yan ta'adan kungiyar Boko Haram sun kashe mutum 69 a kauyen Foduma Kolomaiye mai nisan kilomita 11 daga garin Gazaure da ke karamar hukumar Gubio na jihar Borno a ranar Talata.

Kwakwararan majiyoyi da mazauna garin sun shaidawa Daily Trust cewa yan ta'addan sun kwashe kimanin awanni biyu yayin harin kafin suka tafi.

Bayan mutanen da suka kashe, rahotanni sun ce maharan sun kashe kimanin shanu 300 kuma suka sace guda 1,000.

An gano cewa yan ta'addan sun kai hari a garin ne awanni 24 bayan sun kaiwa matafiya hari a babban titin Monguno.

'Yan Boko Haram sun kashe mutum 69 a wani kauye a Borno
'Yan Boko Haram sun kashe mutum 69 a wani kauye a Borno. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Mazauna garin da suka yi magana da majiyar Legit.ng sun ce mutane da yawa sun jikkata.

Daya daga cikin majiyoyin ya ce akwai mutane da dama da aka nema aka rasa bayan harin.

Dukkan kokarin da aka yi na ji ta bakin mai magana da yawun rundunar sojoji, Col Sagir Musa ya ci tura.

Bai daga wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba misalin karfe 10.09 na daren jiya.

Amma majiya daga daya daga cikin kungiyoyin kasa da kasa da ke aiki a Arewa maso gabashin Najeriya, shugaban kungiyar yan banga da wani mai sharhi kan harkokin yau da kullum sun tabbatar da afkuwar harin na Gubio.

Daya daga cikinsu ya ce, "Wannan shine hari mafi muni a baya bayan nan, yanayin inda garin ya ke ya saka masu aikin jin kai suna samun wahala wurin zuwa kai dauki."

"An kashe mutane da dama wasu kuma har yanzu ba a gansu ba domin maharan sun kai farmaki ne da tsakar rana suka zagaye garin sannan suka bude wuta," in ji shi.

A bangarensa, dan bangan ya ce an kirka gawarwaki 69 banda mutanen da har yanzu ba a gansu ba.

"Za a samu karin bayani game da harin a gobe (Talata)," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel