Gwamnatin kasar Jamus ta baiwa Najeriya gudunmuwar €26m (N11.3bn)

Gwamnatin kasar Jamus ta baiwa Najeriya gudunmuwar €26m (N11.3bn)

- Bayan kudin da gamayyar Turai ta baiwa Najeriya, kasar Jamus ta kara da tukwici

- Jamus ta yi bayanin yadda za'a kashewa yan yanki guda a Najeriya kudin

- Angela Merkel ta nada kudin ne domin yakar illar cutar Korona kan al'ummar Najeriya

Gwamnatin kasar Jamus karkashin jagorancin Cansala Angela Merkel ta taimakawa Najeriya da kudi Yuro milyan 26 wanda yayi daidai da bilyan 11.3 a kudin Najeriya, Punch ta ruwaito.

Ofishin jakadancin kasar Jamus dake nan Najeriya a jawabin da ya saku ya ce an bada gudunmuwar ne domin taimakawa Najeriya wajen yakar cutar Coronavirus da kuma karfafa alaka da kasar.

Jawabin ya kara da cewa an bada wannan kudin ne domin jinkai ga al'ummar Arewa maso gabas musammman jihohin Yobe, Adamawa da Borno.

KU KARANTA: An fara damuwa kan yadda mutane 50 suka mutu a Jos cikin yan kwanaki

Gwamnatin kasar Jamus ta baiwa Najeriya gudunmuwar €26m (N11.3bn)
Buhari da Merkel
Asali: Facebook

Wani sashen jawabin yace, "Jamus ta cigaba da bada gudunmuwar jinkai a Borno, Yobe da Adamawa domin taimakawa gwamnatin Najeriya wajen kula da wadanda ka iya shiga cikin halin kunci ta hanyar sama musu tallafi."

"Gwamnatin kasar Jamus tana mai bada gudunmuwar €26m matsayin jinkai ga al'ummar Arewa maso gabashin Najeriya da kuma yankunan dake makwabtaka da Chadi, Nijar da Kamaru."

Jamus ta bayyana filla-filla yadda za'a raba wannan kudi tsakanin kungiyoyin tallafi daban-daban maimakon mikawa gwamnati.

Ta ce za'a baiwa shirin majalisar dinkin duniya na bada tallafin abinci a Najeriya €8m, za'a baiwa kungiyar Red Cross ICRC €7m, za'a baiwa kungiyar abinci da aikin noma na majalisar dinkin duniya €5m.

Sauran da za'a baiwa sune kungiyar Caritas International €3.5, sannan Asusun lamunin jinkai a Najeriya €2.5.

Legit ta kawo muku rahoto ranar 14 ga Afrilu cewa kungiyar hadakar kasashen nahiyar Turai (EU) ta bawa Najeriya tallafin Yuro miliyan hamsin (£50m) domin yaki da annobar cutar covid-19.

Shugaban tawagar wakilan EU, Ambasada Ketil Karlsen, ne ya sanar da hakan yayin ziyarar da suka kai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa ranar Talata.

Yayin ziyarar, tawagar wakilan ta mika sakon jinjinar EU ga shugaba Buhari a kan kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke yi na yaki da annobar covid-19.

DUBA NAN: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel