COVID-19: Kano za ta bude masana'antu

COVID-19: Kano za ta bude masana'antu

- Gwamna Abudullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bukaci mamallakan manyan masana'antun jihar da su fidda sabbin tsare-tsare

- Gwamnan ya tabbatar da cewa za a yi amfani da sabbin tsare-tsaren wajen sake bude masana'antun jihar

- Ya ce akwai bukatar a gaggauta bude su don shanye illar da korona za ta iya yi wa tattalin arzikin jihar

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci masu manyan masana'antun jihar da su gaggauta miko tsare-tsaren sake budesu a jihar.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya fitar a ranar Litinin, jaridar The Punch ta ruwaito.

Takardar ta ce, Ganduje ya bada wannan umarnin a yayin taro na musamman da ya yi da manyan masu masana'antu na jihar.

Ya ce an yi taron ne don shirya yadda za a dakile kalubalen da ake shirin fuskanta sakamakon annobar korona.

"A halin yanzu, muna bukatar sabbin tsare-tsare da za mu yi amfani da su wurin bude masana'antun ba tare da wani hatsari ga rayukan ma'aikata ba.

"Ina da tabbacin za a fitar da sabbin tsare-tsaren nan ba da dadewa ba don ganin hanya mafi sauki da za mu fuskanci kalubalen da ke gabanmu," Ganduje yace.

Taron ya samu halartar wakilai daga kungiyar masu manyan masana'antu ta Najeriya, kungiyar kasuwanci, masana'antu, hakar ma'adanai da noma da kiwo ta jihar Kano.

COVID-19: Kano za ta bude masana'antu
COVID-19: Kano za ta bude masana'antu. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, a kalla kashi 60 daga cikin mace-macen jihar Kano na da alaka da annobar korona, jami'ai suka sanar.

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana hakan a yayin bayanin inda aka kwana a gaban kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa a ranar Litinin.

Jihar yankin arewa maso yamman ta fuskanci yawaitar mace-mace a jihar, kusan rayuka 979 da suka hada da na manyan sarakuna, ma'aikatan lafiya da manyan malamai.

Kamar yadda ministan yace, kashi 50 zuwa 60 na mace-macen na da alaka da cutar korona. Hakan yana nufin 490 zuwa 587 na mutanen da suka rasu an gano cutar coronavirus ce ta kashesu.

Binciken farko ya bayyana cewa, wasu daga cikin mamatan sun rasa rayukansu ne sakamakon cutar zazzabin cizon sauro ko sankarau, gwamnatin jihar ta sanar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel