Allah mai iko: Likitoci sun cire cajar waya daga mafitsarar majinyaci

Allah mai iko: Likitoci sun cire cajar waya daga mafitsarar majinyaci

- Wani bawan Allah ya shiga asibiti a India inda ya sanar da likitoci cewa ya hadiye cajar waya kacokan

- Bayan duba cikin bawan Allah, likitocin sun yi mishi aiki amma basu samu cajar a cikinsa ba sai a mafitsararsa

- An cire cajar don a halin yanzu yana samun sauki, amma likitoci sun tabbatar da cewa ta hudar mazakutarsa ya saka cajar

Likitoci a kasar India sun sha mamaki bayan da suka cire cajar waya mai tsawon kafa biyu daga mafitsarar wani mutum mai shekaru 30 bayan fara bude cikinsa da suka yi.

Majinyacin wanda a halin yanzu ake bincikar lafiyar kwakwalwarsa, ya sanar da likitocin cewa ya hadiye cajar ne ta bakinsa amma sai suka gano cewa ta mazakutarsa ta shiga.

Allah mai iko: Likitoci sun cire cajar waya daga mafitsarar majinyaci
Allah mai iko: Likitoci sun cire cajar waya daga mafitsarar majinyaci. Hoto daga Wallie Islam
Asali: Facebook

Daya daga cikin likitocin da ya yi wa mutumin aiki, Wallie Islam ne ya wallafa labarin a Facebook. Ya ce majinyacin ya dinga korafin ciwon ciki sannan akwai lokacin da ya hadiye amsa kuwwar waya.

"Abun mamaki. Bayan shekaru 25 da na kwashe ina aiki, na ci gaba da jin mamaki tare da tsananin firgici a irin wadannan al'amura inda ake kalubalantar kwarewata," Islam ya wallafa a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni.

Islam ya ce, sun duba bayan gidan mutumin tare da karin wasu bincike amma ba su samu komai ba. Har da suka bude cikin mutumin, babu cajar.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Na yi mishi aiki amma ban samu komai a cikin cikinsa ba. Amma kuma sai ga doguwar wayar caji a mafitsararsa. Dukkanku za ku iya hasashen ta inda ta shiga. Ta shiga ne ta hudar mazakutarsa," Islam ya rubuta.

Mutumin ya sanar da likitoci cewa ta bakinsa wayar cajar ta shiga amma komai dangane da bayanai sun nuna cewa ta mazakutarsa ta shiga.

"Shekaru na 25 ina yin aiki amma wannan ne lokaci na farko da na fara ganin al'amari irin haka a dakin tiyata," Islam yace.

Akwai yuwuwar cewa mutumin yana Istimna'i ne ta hanyar tura abubuwa ta mafitsararsa.

"Mutumin ya zo mana a kwanaki biyar da suka gabata bayan ya saka cajar. Ya dinga maimaita cewa hadiyeta yayi. Ba mu taba tsammanin cewa babban mutum zai yi karya ba," cewar Islam.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel