Zargin damfara: Sanata ya yi barazanar maka hadimar Buhari a kotu

Zargin damfara: Sanata ya yi barazanar maka hadimar Buhari a kotu

- Sanata Peter Nwaoboshi ya ce zai maka hadimar Shugaba Buhari, Lauretta Onochie a gaban kuliya

- Sanatan ya fitar da wannan barazanar ne ta hannun lauyoyinsa tun kafin majalisar dattijai ta ba wa jami'an tsaro damar bincikarsa

- Wata majiya ta tabbatar da cewa, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya bada umarnin bincikar sahihancin wasikar

Sanata Peter Nwaoboshi ya yi barazanar maka mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin yada labarai, Lauretta Onochie a gaban kuliya.

Nwaoboshi ya yi wannan barazanar ne tun kafin majalisar dattawa ta ba jami'an tsaro damar bincikar zargin takardar bogi da aka fitar daga mataimakin shugaban majalisar a kan bincikar ministan yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio.

A wata wasika da Nwaoboshi ya fitar ta hannun lauyansa, ya bai wa hadimar sa'o'i 48 da ta janye tsokacin da ta yi a kan kwangilar yankin.

A wasikar mai kwanan wata 9 ga Yunin 2020, wacce Bwala and Co da ke Crystal Chambers da Daniel Hassan Bwala suka mika ga Onochie, sun lissafo dukkan abubuwan da Nwaoboshi ke zarginta da su.

Wata majiya ta sanar da cewa shugabannin majalisar dattijan sun bai wa jami'an tsaro umarnin bincike a kan wasikar.

Zargin damfara: Sanata ya yi barazanar maka hadimar Buhari a kotu
Zargin damfara: Sanata ya yi barazanar maka hadimar Buhari a kotu. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Litinin ta kori karar da tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, wacce ke bukatar dakatar da bincikar zargin wata almundahanar filaye da masarautar jihar Kano ta yi.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, a ranar 6 ga watan Maris din 2020 ne tsohon basaraken ya tunkari kotun da bukatar cewa a dakatar da Ganduje, antoni janar da kuma shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar a kan bincikarsa.

Korafin ya bukaci kotun da ta dakatar da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano da shugabanta, Muhyi Rimingado, da ya dakata da bincikarsa har sai an kammala shari'ar farko.

Alkali mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ya yanke hukuncin cewa, hukumar ba ta take wani hakki na tsohon basaraken ba na bincikarsa a kan zargin da ake masa.

Daga nan Allagoa ya yi watsi da karar, tare da tabbatar da cewa babu wani hakkin na Sanusin da aka yi wa karantsaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel