Gwamnatin Zamfara ta yi murnan cika makonni biyu babu mai Korona a jihar

Gwamnatin Zamfara ta yi murnan cika makonni biyu babu mai Korona a jihar

Gwamnatin jihar Zamfara a ranar Talata ta yi murnar cika makonni biyu cir ba'a samu mai cutar Coronavirus (COIVD-19) ba a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kwamitin yaki da COVID-19, wanda shine Kakakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Nasiru Magarya, ya ce an samu nasaran haka ne bisa jajircewan masu ruwa da tsaki.

A jawabin da sakataren yada labaran kwamitin, Malam Mustafa Jafaru Kaura, ya ce Alhaji Magarya ya bayyana hakan ne a Gusau yayinda ya karbi gudunmuwar sabulun wanke hannu guda 36,000 da kungiyar Sightsavers International ta bada.

KARANTA: Daga karshe, kungiyar kasuwancin duniya ta amince da zabin Buhari, Ngozi Okonjo Iweala

Yace: "Wannan abin cigaba ne, dubi ga yadda masu ruwa da tsaki ke bada gudunmuwarsu wajen yakan wannan annobar."

"Ina amfani da wannan damar ina bayyana cewa kawo jiya Litinin, jihar tayi murnar cika kwanaki 14 babu sabon mai cutar COVID-19."

"Cibiyoyin killace masu cutar da gwamnatin jihar ta kafa zasu cigaba da kasancewa a kulle."

Amma ya ce duk da nasarar nan da aka samu, gwamnatin jihar ba zata yi kasa gwiwa ba har sai lokacin da aka bibiyi dukkan wadanda sukayi mu'amala da sanannen mai cutar.

Magarya ya mika godiyarsa ga kungiyar bisa gudunmuwarsu kuma ya yi alkawarin za'a yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata.

Gwamnatin Zamfara ta yi murnan cika makonni biyu babu mai Korona a jihar
Isolation
Asali: UGC

Bayan kimanin mako daya da karewa cutar Korona a jihar Kebbi, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da samun bullar cutar a jihar Kebbi.

A jihar Sokoto kuwa, kwanaki biyu kacal bayan sanar da karewar cutar, an samu karin mutane 12 sabbin kamuwa da cutar.

Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cutuka masu yaduwa (NCDC) ta bayyana ranar 6 ga Yuni, an samu sabbin bulla goma sha daya (11) a jihar Sokoto, yayinda aka samu sabbin bulla biyu (2) a jihar Kebbi.

Ma'aikatar lafiyar jihar Sokoto ta bayyana cewa Almajiran da aka kawo daga jihar Kaduna 33 da aka samu sabbin masu cutar a jihar.

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel