Kwamishinoni uku sun harbu da korona a Gombe

Kwamishinoni uku sun harbu da korona a Gombe

Kwamishinoni uku sun kamu da cutar coronavirus (COVID-19) a jihar Gombe kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kwamishinan labarai da al'adu na jihar, Ibrahim Alhassan ne ya sanar da manema labarai a ranar Talata.

Ya ce an gano kwamishinonin sun harbu da kwayar cutar ne bayan an yi wa kwamishinoni 21 na jihar da hadiman gwamna gwaji.

Alhassan ya kuma tabbatar da cewa daya daga cikin hadiman gwamnan da 'yan majalisar jihar Gombe 5 sun kamu da kwayar cutar ta korona.

Kwamishinoni uku sun harbu da korona a Gombe
Kwamishinoni uku sun harbu da korona a Gombe. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya ce, "A cikin kwamishinoni 21, mun samu uku da suka kamu da cutar. A cikin mashawartan gwamna na musamman, mun samu mutum daya.

"A cikin 'yan majalisun jiha, mun samu mutum biyar. Wannan shine bayanin sakamakon gwajin da aka yi wa jami'an gwamnati."

Kwamishinan ya koka da cewa annobar ta riga ta shiga cikin al'umma kuma an fara ganin yaduwar ta a cikin mutane.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta tabbatar dukkan jami'an ta sunyi gwajin ne domin ya zama abin koyi ga sauran mutane.

Ya ce, "Ya zama dole a hada hannu wuri guda domin yaki da wannan annobar. A yau, sakatarorin dindindin da dukkan direktocin ma'aikatun gwamnati da hukumomi suna gwajin."

Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 a jihar, Farfesa Idris Muhammad shima ya bayar da bayani kan halin da ake ciki a jihar.

Ya ce gwamnati ta yi wa mutum 609 gwaji cikin kwanaki hudu kuma 63 daga cikinsu sun harbu da kwayar cutar.

Farfesa Muhammad ya tabbatar da cewa wasu daga cikin kwamishinoni da 'yan majalisa suna daga cikin wadanda suka kamu da cutar.

Ya yi kira ga mazauna jihar su cigaba da bawa kwamitin hadin kai domin ganin an dakile yaduwar annobar a jihar.

Shugaban kwamitin ya shawarci mazauna jihar musamman wadanda suke muhimman ayyukan yau da kullum su mika kansu ayi musu gwaji.

A cewarsa, mutum 234 ne suka kamu da cutar a jihar baki daya, daga cikinsu 134 sun warke yayin da 33 suna nan suna karbar magani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel