Yanzu-yanzu: Shugaban kasar Burundi ya mutu

Yanzu-yanzu: Shugaban kasar Burundi ya mutu

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya mutu sakamakon ciwon zuciya, a cewar gwamnatin kasar.

A jawabin da aka saki ta shafin Tuwita, gwamnatin ta sanar da cewa shugaban kasarta ya mutu yana mai shekaru 55.

Marigayin ya mutu ne a asibitin Karusi bayan fama da ciwon zuciya a ranar 8 ga Yuni, jawabin yace.

An kwantar da shi ne a asibiti ranar Asabar kuma ya fara samun sauki amma ranar Litinin jikin ya kara tsauri ya samu bugun zuciya kuma ya kwanta dama, BBC ta hakaito.

Pierre Nkurunziza wanda ya kasance kan mulki tun shekarar 2005 na gab da sauka daga mulki a watan Agusta bayan Evariste Ndayishimiye, ya lashe zaben shugabancin kasar a ranar 20 ga Mayun 2020.

Yanzu-yanzu: Shugaban kasar Burundi ya mutu
Yanzu-yanzu: Shugaban kasar Burundi ya mutu
Asali: UGC

Za ku tuna lokacin da marigayi shugaban Pierre Nkurunziza ya yi abin mamaki na bayyana kudirin sauka daga mulki duk da doka ta bashi damar cigaba da zama har shekarar 2034.

Pierre Nkurunziza ya ce ba zai yi takara a zaben da akayi watan Mayu ba kuma ya cika alkawarinsa, TRT ta ruwaito.

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel