Sojoji 45 sun bace, 6 sun mutu yayinda yan Boko Haram suka kai hari

Sojoji 45 sun bace, 6 sun mutu yayinda yan Boko Haram suka kai hari

Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka jami'an Sojin Najeriya shida yayinda suka kai mumunan hari barikin Soji a Arewa maso gabas, majiyoyi daga gidan Soja sun bayyana ranar Lahadi.

Mayakan kungiyar ISWAP cikin motocin yaki sun kai hari ne garin Auno, wani kauye dake da nisan kilomita 25 da birnin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

"Mun yi rashin Sojoji shida a harin da yan ta'addan suka kai misalin karfe 6:30 na yamma ranar Asabar," wani jami'in soja ya bayyanawa AFP.

DUBA NAN: Allah kadai zai sakawa Abacha kan yadda ya sauya Najeriya - Al-Mustapha

Yan ta'addan sun galabi sojin a artabun tsawon awa biyu da aka gwaza kuma hakan ya wajabtawa Sojin janyewa kuma suka arce, wani jami'in sojan ya laburta.

Yan ta'addan sun sace makamai kuma suka kona gidaje kafin wasu sojojin suka fitittikesu.

"Har yanzu ana neman Sojoji 45 da ba'a san inda suke ba amma muna kyautata zaton sun arce ne lokacin harin kuma har yanzu basu dawo ba," Majiya na biyu ya bayyana.

Hukumar Soji ta ki tsokaci kan lamarin.

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Garin Auno na da nisan kilomita 25 da Maiduguri kuma kilomita 120 da jihar Yobe. Wannan ba shi bane karo na farko da yan ta'addan zasu kai hari.

Sun dade suna kaiwa garin hari inda suke kashe Sojoji da sace matafiya.

A watan Febrairu, yan ta'addan ISWAP sun kashe akalla matafiya 30 da Sojoji suka hana shiga Maiduguri daga garin Auno cikin dare.

Rikicin Boko Haram wanda aka kwashe shekaru goma ana fama ya hallaka akalla rayukan 36,000 kuma ya kori akalla milyan 1.8 daga muhallansu a Arewa maso gabacin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa dakarun sojin dake Arewa maso gabas sun hallaka yan Boko Haram 1,429 cikin watanni biyun da suka gabata.

Hakazalika an damke masu kaiwa yan ta'addan rahotannin leken asiri 166.

Buratai ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari ranar Litinin 8 ga watan Yuni, 2020 inda ya ce ana samun gagarumin nasara wajen kawar da yan ta'addan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel