Kan sabani, Uwargida ta yiwa mijinta wanka da tafasasshen ruwan zafi

Kan sabani, Uwargida ta yiwa mijinta wanka da tafasasshen ruwan zafi

Ana neman wata uwargida mai matsakaicin shekaru a garin Yenoguwa, jihar Bayelsa, bayan ta yiwa mijinta wanka da tafasasshen ruwan zafi bayan dan sabanin da suka samu tsakaninsu.

Mijin mai suna, Mr. Oyinkro Miebode, yana bacci ne cikin dakinsu dake unguwar Kpansia na jihar da safiyar 3 ga Yuni inda matarsa ta ji masa mumunan raunin kuna da ruwan zafi.

A hirar da yayi da jaridar Vanguard, ya ce sun fara samin sabani ne da yammacin 2 ga wata inda ya waska mata mari sau biyu saboda ta dura masa ashariya kawai don ya zo karbar wayarta a hannunta don ajiye mata kamar yadda suka saba.

Ya ce ya kan amshi wayanta misalin karfe takwas na dare ya tafi gida saboda za tayi dare kafin ta dawo daga aiki kuma akwai yan daba masu kwace waya a lokacin.

Laifinsa shine sabanin karfe takwas da sukayi yarjejeniyar zai zo, sai ya je kafin lokacin ya jira ta.

A bayaninsa, ya ce yayinda ya tashi aiki karfe 6, sai maigidanshi ya rage masa hanya kuma ya ajiyeshi inda zasu hadu, sai ya jirata a wajen zuwa karfe 8.

Yayinda yake jiranta, kawai sai ya ganta misalin karfe 7 tana wucewa. Sai ya ruga ya sameta don fada mata gashi ya iso amma ta nuna bacin rai saboda ya zo da wuri.

Kan sabani, Uwargida ta yiwa mijinta wanka da tafasasshen ruwan zafi
Kan sabani, Uwargida ta yiwa mijinta wanka da tafasasshen ruwan zafi
Asali: Facebook

Yace: "Abin ya bani mamaki, sai na tambayeta menene abin haushi don na zo da wuri.....Sai ta fara tuhumata da cewa ina bibiyanta. Bata daina dura min ashariya ba har sai da muka isa gida."

"Ko da muka isa gida ma ta cigaba. Sai cikin fushi na waska mata mari biyu kuma na umurceta ta shiga daki ta kwanta."

"Ina kwance kan kujera a daki kawai ta yi min wanka da ruwan zafi."

Wani wanda ke zaune a gidan ya tabbatar da labarin inda ya shaida abin da ya faru.

Yace: "Bayan sun gama sa'insan sai ya tafi ya kwanta. Daga baya ta fara tambayar yar'uwarsa shin akwai kalanzir cikin risho. Yar'uwar ta fada mata babu."

"Sai ta fita wajen ta sayi Kalanzir. A tunanina tana kokarin daura ruwan zafi ne domin wanka ko tuka teba. Har na sanar da ita lokacin da ya fara tafasa."

"Sai ta zuba ruwan zafin cikin karamin baho ta shiga daki inda yake ta watsa masa. Kawai sai ya tashi a rikice yana iwu yana sosa jikinsa ba tare da sanin fatar jikinsa yake yayewa ba."

Tana aikata hakan ta arce daga gidan kuma an bazama nemanta yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel