Da duminsa; Kotu ta yi watsi da karar kungiyar dattawan Kano na bukatar rusa sabbin masarautun Kano

Da duminsa; Kotu ta yi watsi da karar kungiyar dattawan Kano na bukatar rusa sabbin masarautun Kano

Babbar kotun jihar Kano ta yi watsi da karar da kungiyar dattawan Kano karkashin jagorancin tsohon dan takarar kujeran shugaban kasa, Alhaji Bashir Tofa, ta shigar kan sabbin Masarautun Kano a gwamnatin jihar ta kirkiro.

Kungiyar ta dattawan Kanon ta bukaci kotun ta rusa sabbin Masarautun biyar saboda hakan ya sabawa doka.

Alkalin kotun, N.S Umar ya yi watsi da karar ne bayan Antoni Janar na jihar Kano, Ibrahim Muktar, ya kalubalanci hurumin Alhaji Bashir Tofa na shigar da karar.

Hakazalika an rusa karar saboda rusa masarautun na iya tayar da tarzoma a jihar.

Hadimin gwamnan jihar Kano kan labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook da safiyar Talata, 9 ga watan Yuni, 2020.

DUBA WANNAN: Kan sabani, Uwargida ta yiwa mijinta wanka da tafasasshen ruwan zafi

Da duminsa; Kotu ta yi watsi da karar kungiyar dattawan Kano na bukatar rusa sabbin masarautun Kano
sabbin masarautun Kano
Asali: Twitter

Yace: "A jiya litinin 8 ga watan June, wata kotu karkashin jagorancin Mai Shariah N.S Umar ta yi watsi da karar da su Alhaji Bashir Tofa su ka kai inda suke neman kotun ta rusa sababbin masarautu guda biyar da Gwamnatin Jiha ta yi karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR.

Babban A na jihar Kano wato Barrister Ibrahim Mukhtar ne ya kalubalanci karar akan cancantar masu karar akan neman a soke masarautun.

Kotun ta kara da cewa karar zata iya bude wani sabon shafi na kalubale kala kala aduk wani mataki da aka dauka akan masarautun nan gaba. Don haka kotun tai watsi da wannan kara kuma masarautun 5 suna nan daram dam dam."

Mun kawo muku a watan Junairu cewa Alhaji Bashir Tofa tare da wasu dattawan Kano 19 suka shigar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kan kafa sabbin masarautu.

Wadanda aka shigar kotu sune: Gwamnan jihar Kano, Kakakin majalisar dokokin jihar, Majalisar dokokin jihar da kanta, babban Lauyan jihar Kano, sarkin Rano, Tafida Abubakar-Ila (Ya rasu); sarkin Gaya, Ibrahim Abdulkadir-Gaya; sarkin Karaye, Dakta Ibrahim Abubakar II; da sarkin Bichi (Na Kano a yanzu), Aminu Ado-Bayero, da masarautar Kano.

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel