Obasanjo ya yi kashedi game da matsalar karancin abinci da za a fuskanta bayan annobar korona ta gushe

Obasanjo ya yi kashedi game da matsalar karancin abinci da za a fuskanta bayan annobar korona ta gushe

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya yi gargadi game da matsalar karancin abinci da za a fuskanta a Najeriya da sauran kasashen nahiyyar Afirka bayan annobar cutar korona ta gushe.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Obasanjo ya bukaci gwamnatocin kasashen da su tashi tsaye wajen fuskantar kalubalen da ke ci gaba da tunkaro su.

Tsohon shugaban kasar ya nemi ‘yan Najeriya da su dauki batun abin da zai faru bayan gushewar annobar korona da mahimmancin gaske.

Yana mai cewa, bayan likafar annobar korona ta gama cin kasuwarta, za kuma ta bude kofar matsalar karancin abinci a Nahiyar Afirka.

Tsohon shugaban kasar Najeriya; Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban kasar Najeriya; Olusegun Obasanjo
Asali: UGC

Dattijon ya fadi hakan ne a harabar Laburarensa na Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke birnin Abeokuta a jihar Ogun.

Furucin tsohon shugaban kasar ya zo ne yayin da ya kaddamar da shirin fara aikin noman kifi, a karshen mako da ya gabata.

KARANTA KUMA: Kamfanoni 47 sun biya masu hannayen jari N1.1trn a 2019

Haka kuma Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar da ke kula da kasuwanci ta duniya, WTO sun yi irin wannan gargadi na tsohon shugaban Najeriya.

Sun yi kashedin cewa akwai yiwuwar duniya za ta fuskanci karancin abinci idan mahukunta suka gaza shawo kan annobar korona.

Hukumomin biyu sun ce dokar kulle da gwamnatoci a duniya suka sanya ta yi mummunar takaita hada-hadar kayan abinci a kasuwannin duniya.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Haka zalika dokar kulle da aka shimfida a kasashen duniya saboda takaita yaduwar cutar korona, ta kara haifar da karanci da tsadar abinci a wasu wurare.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutum 315 da suka kamu da cutar korona a Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa a Najeriya ta fitar da misalin karfe 11.41 na daren ranar Litinin 8 ga Yuni na shekarar 2020.

Alkalluman da Hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa, jimillar wadanda suka kamu da cutar korona a kasar ta kai dubu goma sha biyu da 801.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel