An dakatar da dokar cin gashin kan majalisu da bangaren shari’ar jihohi bayan ganawar Buhari da gwamnoni

An dakatar da dokar cin gashin kan majalisu da bangaren shari’ar jihohi bayan ganawar Buhari da gwamnoni

- Gwamnoni sun ji sa'ida bayan dakatar da dokar cin gashin kan majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi

- Gwamnan Ekiti ya ce Buhari ya jingine dokar ne domin warware duk wata tufka da warwara da ke cikin sabuwar dokar

- Buhari ya dakatar da fara aiki da dokar bayan gwamnoni sun nuna damuwa da rashin jin dadi matuka a kan sabuwar dokar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da fara aiki da sabuwar dokar nan wadda ta bai wa majalisu da bangaren shari’a na Jihohi ikon cin gashin kan su a fannin sha'anin kudi.

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, wanda kuma ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, shi ne ya bayyana hakan cikin birnin Abuja a ranar Litinin.

Furucin Dakta Fayemi ya zo ne bayan ganawar gwamnonin da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da wasu ministoci.

An dakatar da dokar cin gashin kan majalisu da bangaren shari’ar jihohi bayan ganawar Buhari da gwamnoni
An dakatar da dokar cin gashin kan majalisu da bangaren shari’ar jihohi bayan ganawar Buhari da gwamnoni
Asali: UGC

Fayemi ya ce shugaba Buhari ya dakatar da fara aiki da sabuwar dokar ne saboda damuwa da gwamnonin suka nuna kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

Gwamnonin sun nuna damuwa kan dokar da za ta ba wa majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi damar samun kudadensu kai-tsaye ba tare da ya bi ta hannun gwamnoni ba.

KARANTA KUMA: 12 ga watan Yuni: Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun ranar Juma'a

Gwamnonin su nuna cewa sabuwar dokar mai suna 'The Executive Order 10, 2020', akwai wasu wurare da kundin tsarin mulki na kasar nan ya kamata ya yi bita a kansu.

Bayan sauraron korafe-korafensu, Fayemi ya ce Buhari ya dakatar ko kuma zai yi jinkirin tilasta fara aiki da dokar tukunna, har sai an warware wuraren da kulli ya cukurkude.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2020, shugaban Najeriya ya rattaba hannu a kan dokar da ta ba majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi damar cin gashin kansu.

A karkashin wannan sabuwar doka, Buhari ya ba wa Ofishin Akanta Janar na kasa umarnin cire wa majalisun dokoki da bangaren shari’a kudaden su daga asusun duk wata jiha da ta ki bin wannan umarni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel