Kano da wasu jihohi 4 da suka gaza bayyana kudin da suka kashe kan gwajin korona

Kano da wasu jihohi 4 da suka gaza bayyana kudin da suka kashe kan gwajin korona

Jihohin Kano, Kwara, Ogun, Edo da Oyo sun gaza bayyana adadin kudin da suka kashe wurin yin gwajin kwayar cutar coronavirus a jihohin su.

Makonni kadan da suka gabata, an bayyana cewa jihar Legas ta kashe Naira miliyan 800 a kan gwajin na COVID-19.

Kwamishinan Lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya ce a kalla a kan kashe kimanin N40,000 zuwa N50,000 a kan kowanne gwajin COVID-19 a jihar a wannan lokacin.

Sai dai yunkurin da aka yi na gano adadin kudaden da wasu jihohi kamar Kano, Ogun, Kwara, Edo da Oyo suka kashe ya ci tura.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kwara, Rafiu Ajakaye ya ce gwamnatin jihar ba ta karbar kudi daga hannun mutane da aka yi wa gwajin na COVID-19.

Kano da wasu jihohi 4 sun ki fadin adadin kudin da suka kashe wurin yaki da korona
Kano da wasu jihohi 4 sun ki fadin adadin kudin da suka kashe wurin yaki da korona
Asali: Twitter

Ya ce, "Gwamnati ba ta karbar kudin gwaji daga hannun majinyata da aka yi wa maganin COVID-19 a jihar."

Da aka nemi sanin adadin kudin da jihar ta kashe a kan gwaje gwajen, kakakin gwamnan ya ce ba zai iya bayyana wa ba saboda har yanzu ba a gama gwaje gwajen ba.

Gwamnatin jihar Oyo ita ma ta ce ita ke biyan dukkan kudaden gwaji da magungunan mutane 365 da aka ruwaito sun kamu da COVID-19 a jihar.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Sai dai itama ta ce a halin yanzu ba za ta iya bayyana jimillan kudin da aka kashe wurin gwaji da yi wa majinyatan magani ba sakamakon dokar kule da ke hana maaikatan gwamnati zuwa aiki.

Taiwo Adisa, kakakin Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ne ya bayyanawa The Punch hakan a hirar wayar tarho da suka yi a ranar Lahadi.

A bangarenta, gwamnatin Kano ta ce har yanzu ba ta gama kididige adadin kudin da aka kashe wurin gwajin COVID-19 a jihar.

Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na jihar, Dr Tijjani Husain ne ya bayyanawa majiyar Legit.ng haka a hirar tarho a ranar Lahadi.

A jihar Ogun gwamnatin jihar ta ce ba ita ta biya kudin gwaji da magani ba kuma ba majinyata suka biya ba.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Tomi Coker ta ce wasu masu bayar da gudunmawa ne suka biya. Ta ce ba ta san takamammen adadin kudin da aka kashe ba.

Gwamnatin Edo a ranar Lahadi ta ce duk da cewa kudin gwaji da maganin korona yana da yawa, gwamnatin jihar ne ta biya.

Mashawarci ga Gwamna Obaseki a kan Watsa Labarai, Mr Crusoe Osagie ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa ba zai iya cewa ga adadin kudin da aka kashe wurin gwajin ba a hirar tarho da aka yi da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164