Wasu sojojin bogi da suka lakadawa dan sanda duka sun shiga hannu

Wasu sojojin bogi da suka lakadawa dan sanda duka sun shiga hannu

An kama wasu maza biyu, Abdullahi Kabiru da Obare Tunde da suka sanya kayan sojoji kana suka yi wa wani dan sanda mai mukamin constable, Lawrence Awoniyi a Omuo Ekiti a karamar hukumar Ekiti ta Kudu duka.

Mutanen biyu da suka gabatar da kansu a matsayin sojoji masu mukamin kyaftin sun yi wa dan sandan duka ne a ranar 31 ga watan Mayun 2020.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyu sun fito ne daga Omuo Ekiti da ke kauyen Ife Olukotun na jihar Kogi.

Wasu sojojin bogi da suka lakadawa dan sanda duka sun shiga hannu
Wasu sojojin bogi da suka lakadawa dan sanda duka sun shiga hannu. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

The Punch ta ruwaito sun doki dan sandan ne bayan sun hange shi sanye da kayan aikinsa.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Kwamishinan yan sandan jihar Ekiti, Mr Asiquo Amba ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce "mutane biyun da ake zargi sun gabatar da kansu a matsayin sojoji masu mukamin kyaftin daga bataliya ta 44 na jihar Niger.

"Sun ci zalin dan sandan sun masa dukan zauna ka ci doya kuma suka yi barazanar za su fasa kansa da kwalba."

"Daga bisani dan sandan ya gayyato abokan aikinsa inda suka yi nasarar damke wadanda ake zargin.

"Yayin da SARS ke musu tambayoyi, sun amsa cewa su ba sojoji bane kuma kayan da suke sanya da shi na daya daga cikin dan uwansu ne."

Amba ya ce ana cigaba da bincike a halin yanzu domin gano gaskiyar ikirarin da suka yi na cewa kayan sojojin na dan uwansu ne.

Kwamishinan ya kuma ce yan sanda sun kama wani Abdulsalam Olalekan da aka kama yana karyar cewa shi dan yi wa kasa hidima ne a Atinkankan na jihar Ekiti a watan Mayu.

Amba ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya saci hular masu yi wa kasa hidima, takalma da kuma katin shaida na wani Akinlabi Teslimat Damilola da katin shaidar wani Abdulsalam Ibrahim na jami'ar jihar Kebbi.

Ya kara da cewa an mika wanda ake tuhumar hannun 'yan sandan jihar Edo domin cigaba da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel