Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna)

Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna)

- Ruwan sama mai matukar karfi ya yi awon gaba da gidajen wucin-gadi na 'yan gudun hijira a Maiduguri

- Gidajen na nan a rukunin gidaje masu sauki kudi na Shagari da ke garin Maiduguri a jihar Borno

- 'Yan gudun hijarar sun yi kira ga hukumomi da su tallafa don gyara musu mazauninsu da ruwan ya kwashe

Mamakon ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen wucin-gadi na 'yan gudun hijira da ke sansaninsu a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Sansanin na nan a Low-cost B Shagari Housing Estate. Akwai gidaje a kalla 40 da aka kafa a sansanin mai zaman kansa tun a shekarar da ta gabata.

Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna)
Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna). Hoto daga Channels Tv
Asali: Twitter

Babbar cocin Redeemed Christian Church of God ce ta samar da wadannan gidajen wucin-gadin.

Gagarumar guguwar wacce ta fara da yammaci, ta kwashe gidajen tare da kwashe tantin jama'a.

Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna)
Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna). Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

Duk da babu wanda ya samu rauni a sansanin 'yan gudun hijirar, amma sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin da ya kamata.

Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna)
Ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen 'yan gudun hijira a Borno (Hotuna). Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel