Babban ɗan sanda ya mutu yayin gasar lalata da budurwarsa a Nasarawa

Babban ɗan sanda ya mutu yayin gasar lalata da budurwarsa a Nasarawa

An tsinci gawar wani ɗan sanda mai muƙamin DSP tsirara a ɗakinsa da ke barikin ƴan sanda a ƙaramar hukumar Akwanga na jihar Nasarawa.

Ana zargin DSP Francis Onugha da ake yi wa laƙabi da (Dangote) ya mutu ne bayan kashe dare suna gasar lalata da budurwarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kafin rasuwarsa, shine jami'i mai kula da sashin aikata laifuka (DCO) 1 na yankin Akwanga.

Wani ganau ba jiyau ba ya ce kofar dakin marigayin ɗan sandan a bude ta ke yayin da suka tsinci gawarsa da kumfa na fita daga bakinsa da hancinsa.

Babban ɗan sanda ya mutu yayin gasar lalata da budurwarsa a Nasarawa
Babban ɗan sanda ya mutu yayin gasar lalata da budurwarsa a Nasarawa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya yi iƙirarin cewa wata mata da ba a bayyana sunanta ba ta kwana a ɗakin ɗan sandan amma ta sulale ta fice bayan ta gano ya mutu.

Wata majiya daban ta ce matar ta jefa wayoyinsa biyu cikin ruwa saboda kada a duba wayan a gano lambar ta.

Wasu mazauna unguwar sun ce marigayin DCO ɗin mutum ne mara wasa da aikinsa da ya saba fita da asuba zuwa wurin aiki.

Sun ce a ranar Lahadin da lamarin ya faru, bai fito ya tafi aikinsa da safe kamar yadda ya saba ba har sai lokacin da wani ɗan sanda ya zo duba shi ya gano gawarsa.

Kakakin ƴan sandan jihar Nasarawa, ASP Nansel Rahman ya tabbatar da mutuwar DSP Onugha.

Sai dai ya musanta cewa mamacin ya rasu ne bayan gasar lalata da wata mata.

Acewarsa: "An kai gawar mamacin zuwa babban asibitin garin Akwanga inda za a bincika a gano sanadin mutuwarsa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel