Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa tsohon kwamishanan yan sanda, Abubakar Tsav, rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa tsohon kwamishanan yan sanda, Abubakar Tsav, rasuwa

Allah ya yiwa Mai sharhi kan lamuran yau da kullum kuma tsohon kwamishanan yan sandan jihar Legas, Alhaji Abubakar Tsav, rasuwa, Daily Trust ta ruwaito.

Marigayin ya rasu ne ne da safiyar Litinin, 8 ga watan Yuni, 2020 bayan gajeruwar jinyar da yayi a asibtin tarayya dake Makurdi, jihar Benuwa.

Hadiminsa na musamman, Torkuma Uke, ya tabbatarwa manema labarai labarin mutuwarsa.

Alhaji Abubakar ya kasance dattijon da bai gajiya wajen baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan lamuran da suka shafi kasa, musamman tsaro.

KU KARANTA: Bayan ganawa da Buhari, Buratai ya bayyana adadin yan Boko Haramun da aka kashe cikin wata 2

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa tsohon kwamishanan yan san, Abubakar Tsav, rasuwa
Abubakar Tsav
Asali: Twitter

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A cikin shawarinsa na karshe, Abubakar Tsav, ya ce har yanzu Najeriya bata kai munzalin kirkirar 'yan sandan jiha ba kamar yadda wasu ke bijiro da bukatar yin hakan ba.

Tsohon kwamishinan 'yan sanda, Abubakar Tsav yace"Kirkirar 'yan sandan jiha zai bayar da wata kafa da zata kawo durkushewar Najeriya cikin sauri,"

"ko a halin yanzu gwamnoni basa iya kulawa da jami'an 'yan sanda dake aiki a jihohin su, sannan za su yi amfani da 'yan sandan jiha domin biyan bukatun kansu."

Hakazalika ya yi kira da Buhari ya dauki yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya da matukar muhimmanci.

Ya bayyana haka ne a shekarar 2017 a birnin Makurdi a lokacin da yake taya shugaban kasa murnar zagayowar ranar haihuwar sa da cika shekaru 75 a duniya.

Tsav ya shawarci Buhari “yayi amfani da karfi da karfe wajen yakar cin hanci da rashawa a Najeriya, kada Buhari ya kuskura ya bari a siyasantar da kudirin sa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel