'Yan sanda sun kama wani kirista da ya ke shirin kai wa Musulmai hari a Masallaci

'Yan sanda sun kama wani kirista da ya ke shirin kai wa Musulmai hari a Masallaci

'Yan sandan kasar Jamus sun tsare wani mutum da ake zargi da shirin kashe Musulmai ta hanyar kai musu hari a irin salon da aka kaiwa Musulmai hari a wani Masallaci da ke Christchurch a kasar New Zealand.

Jami'an 'yan sanda masu gabatar da kara ne suka sanar da hakan a ranar Litinin.

Mutumin, mai shekaru 21 dan asalin birnin Hildesheim, ya sanar da shirinsa na kai harin ne a wani boyayyen sako da ya wallafa a yanar gizo, a cewar ofishin 'yan sanda na garin Celle.

Bincike farko - farko da jami'an tsaro suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin "ya dade ya na da tunanin son kai hari tare da kashe mutane da yawa don kawai ya jawo hankalin duniya," a cewar ma su gabatar kara.

Mai laifin ya ambaci sunan mutumin da ya kashe Musulmai 51 a Masallatai biyu da ke Christchurch a watan Maris na shekarar 2019, tare da bayyana cewa ya na sha'awar kai kwatankwacin irin harin.

"Niyyarsa ita ce ya kashe Musulmai,"kamar yadda ma su gabatar da kara su ka sanar.

'Yan sanda sun samu makamai da wasu tarin litattafai da takardun yanar gizo na kungiyar 'yan ta'adda ma su tsaurin ra'ayi da ake kira 'right - wing' a gidan matashin.

'Yan sanda sun tsare shi a ranar Asabar bisa tuhumarsa da laifukan da suka shafi niyyar aikata ta'addanci da kuma bawa 'yan ta'ada gudunmawa ta hanyar sayen makamai.

Kasar Jamus na fuskantar yawaitar kai hare - haren kyamar addini a cikin watanni 12 da suka gabata.

'Yan sanda sun kama wani kirista da ya ke shirin kai wa Musulmai hari a Masallaci
Babban Masallacin Abuja
Asali: Twitter

Ko a cikin watan Fabrairu sai da wani dan ta'adda mai akidun kungiyar 'right - wing' ya kai hari tare da kashe mutane 9 a wata mashaya da wurin shan Shisha a birnin Hanau da ke daura da Frankfurt.

DUBA WANNAN: Buratai ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Kazalika, a cikin watan Oktoba na shekarar 2019, mutane biyu aka kashe a wani hari da aka kai wani gini mallakar mabiya addinin Kirista a garin Halle da ke kusa da Leipzig.

A watan Yuni na shekarar 2019 aka gurfanar da wani mai akidun kungiyar 'right - wing' bisa zarginsa da laifin kisan Walter Luebcke, dan siyasa mai goyon bayan tsarin karbar bakin haure.

Horst Seehofer, ministan cikin gida, ya ce kasar Jamus na fuskantar babbar barazana daga kungiyar ta'addanci ta 'right - wing'.

Ministan ya dauki alkawarin cewa za a bunkasa tsaro domin dakile aiyukan kungiyar tare da kama mambobinsu da ke cikin kasar Jamus.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel