Da duminsa: Likitocin Najeriya zasu tafi yajin aiki ranar Litinin

Da duminsa: Likitocin Najeriya zasu tafi yajin aiki ranar Litinin

Kungiyar manyan Likitocin Najeriya NARD ta yiwa gwamnatin tarayya barazanar tafiya yajin aiki daga ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, 2020.

Shugaban kungiyar likitocin na kasa, Aliyu Sokomba, ya bayyana hakan ne a wasikar da ya aikewa gwamnati mai lamba 2020/070620/246.

Shugaban Likitocin ya ce tafiya yajin aikin ya zama wajibi ne saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen cika alkawuranta wajen inganta albashi da jin dadinsu.

Ya ce muddin suka tafi, sai lokacin da Allah yayi.

Da duminsa: Likitocin Najeriya zasu tafi yajin aiki ranar Litinin
Da duminsa: Likitocin Najeriya zasu tafi yajin aiki ranar Litinin
Asali: UGC

KU KARANTA: An damke mai cutar Korona da ta gudu a daga jihar Imo a jihar Ondo tana sayar da gwanjo

Yace: "Sakamakon wa'adin kwanaki 14 da muka baiwa gwamnatin tarayya kan yajin aikin da zamuyi,.....muna masu sanar da ku cewa dukkan likitocin NARD a asibitocin gwamnatin tarayya da na jihohi za su tafi yajin aiki fari daga karfe 12:00 na daren Litinin, 15 ga Yuni, 2020."

"Ba zamuyi aiki ko daya ba, ko da na gaggawa ne, amma mun togaciye masu kula da masu fama da COVID-19. Mambobin kungiyar da suka hada da dukkan Likitocin digiri na biyu, kananan likitoci.... gaba daya zasu shiga yajin."

"Yana da muhimmanci a samar da mafita ga masu jinya saboda mai gaba daya zamuyi kuma babu ranar dawowa."

"Muna kara jaddada cewa bukatun da muka mikawa gwamnati da yasa zamu tafi yajin aikin nan sun hada; rashin isassun kayayyakin kare kai, dawo da likitoci 26 da aka sallama daga asibitin koyarwan jami'ar Jos, biyansu kudin albashin da aka rike musu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel