Ma'aikatan NDDC 6 sun kamu da cutar korona

Ma'aikatan NDDC 6 sun kamu da cutar korona

Rahotanni da muka samu a yanzu sun bayyana cewa, ma'aikata shida na Hukumar Raya yankin Neja Delta NDDC, sun kamu da cutar korona.

Hukumar ta bayyana hakan cikin wani sako da ta wallafa a ranar Litinin, 8 ga watan Yuni, kan shafinta na Twitter.

Ma'aikatan Hukumar Raya Neja Delta NDDC
Ma'aikatan Hukumar Raya Neja Delta NDDC
Asali: Facebook

KARANTA KUMA: Takunkumin rufe fuska kadai ba ya hana kamuwa da cutar korona - WHO

Sanarwar ta bayyana cewa, jami'an shida da suka kamu ma'aikata ne a ofishin Babban Darektan aikace-aikace na Hukumar, Dr. Cairo Ojougboh.

Sai dai sakamakon gwaji ya nuna cewa, Dr Ojougboh ba ya dauke da kwayoyin cutar kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta bayyana cewa, "A yayin da jami'an Hukumar NDDC suka killace kansu kuma ana ci gaba da yi musu gwajin cutar korona, sakamako ya nuna cewa ma'aikata shida cikin 33 sun kamu da kwayoyin cutar."

"Jami'an shida ma'aikata ne a ofishin Babban Darektan aikace-aikace, Dr Cairo Ojougboh. Sai dai Dr. Ojougboh ba ya dauke da kwayoyin cutar."

Kwanaki goma da suka gabata ne Hukumar NDDC ta ba da umarnin gaggauta garkame ofishinta na makonni biyu bayan mutuwar mukaddashin Daraktan kudi, Ibanga Bassey Etang.

Akwai zaton da ake yi na cewa mukaddashin daraktan hukumar ya mutu ne sakamakon kamuwa da annobar korona.

Hukumar karkashin jagorancin Prof Daniel Pondei, ta fitar da umarnin rufe ofishin makonni biyu rak.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Silas Anyawu, wanda ya sa hannu a kan takardar a madadin hukumar, ya rubuta: "Ina umartar dukkan ma'aikatan hukumar NDDC da su dakata da aiki don rufe ofishin da za a yi na makonni biyu daga ranar 28 ga watan Mayun 2020."

"Hakazalika, dukkan ayyukan hukumar ya tsaya cak har zuwa lokacin da za ta dawo aiki."

"Ana shawartar dukkan ma'aikata da su tabbatar da cewa sun kashe kayayyakin wuta da ke ofishinsu kafin tafiya hutun."

"Da wannan takardar ake umartar shugaban sashen tsaro na hukumar da ya fitar da tsare-tsaren tsaro na hukumar yayin da za a yi feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka a ofishin kafin a dawo."

"Ana ci gaba da umartar ma'aikatan NDDC da su killace kansu na makonni biyu yayin da ake jiran wani umarni daga hukumar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel