Yan sanda sun damke dan bautar kasa da soji biyu na bogi

Yan sanda sun damke dan bautar kasa da soji biyu na bogi

Jami'an Rundunar yan sandan Jihar Ekiti sun damke wani mai suna Abdulsalam Olekan kan laifin satar kayan masu bautar kasa(NYSC).

Wanda ake zargin ya fito a matsayin dan bautar kasa a Jihar.

Abdulsalam, wanda yan sandan SARS suka kama a ranar 10 ga watan Mayu na shekarar 2020, a wani sintiri dasu ka kai a yankin Atikankan na Birnin Ado-Ekiti, ya laburta cewa shi mai bautar kasar bogi ne.

A wani jawabi daga bakin kwamishinan dan sandar jihar, Mista Asuquo Amba, ya tabbatar da cewa Abdulsalam ya laburta cewa ya shiga gidan wani mai suna Abdulsalam Ibrahim ne dake Agbhenebode a Jihar inda ya saci hula da takalmin NYSC.

“Wanda ake zargin ya saci katin zama dan makaranta na Jami’ar Olabisi Onabanjo mai dauke da sunan Akinlabi Teslimat Damilola.

“Sannan ya hada da katin zama dan makaranta na jami’ar Kebbi da kuma katin zama dan bautar kasa duk masu dauke da sunan Abdulsalam Ibrahim.”

“Za’a mika shi ga yan sandan jihar Edo domin karbar hukunci.” Yace.

KU KARANTA: Hankalin ma'aikatar lafiya ya tashi yayinda adadin masu cutar Korona ya zarce adadin gadajen asibiti a fadin tarayya

Yan sanda sun damke dan bautar kasa da soji biyu na bogi
Yan sanda sun damke dan bautar kasa da soji biyu na bogi
Asali: Facebook

Shugaban yan sandan ya kara da cewa sun damke wani Abdullahi Kabiru da Obaro Tunde wadanda suka fito daga kauyen Olukotun dake karamar hukumar Yagba na jihar Kogi.

An kama su da laifin kaima wani dan sanda hari mai suna Awoniyi Lawrence.

Yace: “Wadanda ake zargin masu ikirarin sojoji ne sun kaima dan sandan hari inda suka mai shegen duka sannan suka yi barazanar fasa mai kai da kwalba."

“An damke sune yayinda dan sandan ya yi kururuwar neman agaji."

"A yayin bincike, wadanda ake zargin sun laburta cewa su sojin bogi ne kuma inifom din sojin na dan uwansu ne.”

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel