Hankalin ma'aikatar lafiya ya tashi yayinda adadin masu cutar Korona ya zarce adadin gadajen asibiti a fadin tarayya

Hankalin ma'aikatar lafiya ya tashi yayinda adadin masu cutar Korona ya zarce adadin gadajen asibiti a fadin tarayya

- Najeriya ta fara samun karancin gadajen kwantar da sabbin masu kamuwa da cutar Korona

- Adadin masu cutar ya fi yawa a jihar Legas, Kano da Abuja

- Da yiwuwan nan da yan kwanaki a rasa wurin ajiye mara lafiya

Akwai alamun cewa Najeriya na iya shiga halin kakanikaye cikin yan kwanakin nan masu zuwa sakamakon tashin gwauron zabon da adadin sabbin masu kamuwa da cutar Coronavirus ke yi.

A yanzu, adadin wadanda ke asibiti ya zarcewa adadin gadajen da ake da shi.

Ma'aikatar lafiyar tarayya ta bayyanawa The Punch ranar Juma'a cewa gadaje 6,826 ake da shi a fadin tarayya domin jinyar masu cutar Korona.

A ranar Asabar, adadin wadanda suka kamu a Najeriya ya kai 12,233. Yayinda aka sallami 3,826, 8,065 na kwance asibiti yanzu.

Rahoto ya bayyana cewa tsakanin ranar Juma'a da Lahadi, ba'a samu sabbin gadaje ba duk da cewa adadin sabbin masu kamuwa da cutar ya karu.

Diraktar lamuran Asibitoci na ma'aikatar lafiyar tarayya, Dr Adebimpe Adebiyi, ta bayyanawa jaridar Punch cewa jihar Legas da Kano ke kan gaba wajen rashin gadajen ajiye masu cutar.

Amma birnin tarayya Abuja da jihar Ogun na da isassun gadaje yanzu.

Hankali ma'aikatar lafiya ya tashi yayinda adadin masu cutar Korona ya zarce adadin gadajen asibiti a fadin tarayya
Isolation
Asali: UGC

Za ku tuna cewa kwamishinan lafiyan jihar Legas, Farfesa Akin, ya bayyana cewa nan da makonni uku gadaje zasu kare a jihar muddin aka gaza shawo kan lamarin karuwar da masu cutar keyi.

Hakazalika dirakta janar na hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya Dr Chikwe Ihekweazu, ya yi bayanin cewa saboda karancin gadaje, gwamnatin tarayya ta fara tunanin jinyar mutane a gidajensu.

Bayan haka ya sake bayyana cewa za'a fara sallaman masu cutar Coronavirus ko da gwaji bai nuna sun warke ba, sakamakon sabon binciken kimiyya da aka samu.

Binciken ya nuna cewa za'a iya sallamar masu cutar da suke fama da mura, zazzabi, ciwon jiki ko wasu alamu bayan akalla kwanaki goma suna jinya muddin alamun sun gushe, ko da gwaji bai nuna sun warke ba.

Bugu da kari, kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da COVID-19 ta bayyanawa otal-otal da shugabannin makarantun kwana su shirya saboda akwai yiwuwan fara kwantar da masu cutar Korona a wurinsu.

Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel