FG ta bayyana matsayin Buhari a kan makomar 'yan N-Power da aka fara dauka
- Gwamnatin tarayya (FG) ta ce bata da niyyar bayar da aiki ga matasan da aka fara dauka aikin sa kai na wucin gadi a karkashin shirin N-Power
- Ma'aikatar kula da harkokin hidimtawa 'yan kasa ta karyata labarin da ake yadawa a kan cewa shugaba Buhari zai sanar da bayar da aiki ga matasan a ranar 12 ga watan Yuni
- A kwanakin baya ne minista ma'aikatar, Sadiya Umar Farouq, ta ce za a yaye matasan tare da daukan wasu sabbi
Gwamnatin tarayya ta mayar da martani a kan rahotannin da ake yadawa a kan cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai dauki matasan da ke cin moriyar shirin N-Power aiki bayan karewar wa'adinsu na shekaru biyu.
Rhoda Iliya, mataimakiyar darektan yada labarai a ma'aikatar walwala, bayar da tallafi da jin kai, ta yi watsi da rahotannin tare da bayyanasu a matsayin labaran kanzon kurege, marasa tushe.
Ma'aikatar ta bayyana haka ne biyo bayan labarin da ake yadawa a dandalin sada zumunta a kan cewa shugaba Buhari zai sanar da daukan 'yan N-Power rukunin 'A' aiki a jawabin da zai gabatar a ranar 12 ga watan Yuni.
A cikin labarin da ake yadawa, an nuna cewa shugaba Buhari zai sanar da daukan matasan aiki a matsayin tukuicin kammala aikin wucin gadi na shekara biyu da su ka yi wa gwamnatin tarayya.
A cikin sanarwar, ma'aikatar harkokin hidmtawa 'yan kasa ta ce a kafofinta na yada labarai ne kadai za a fitar da duk wata sanarwa da ta shafi ma su cin moriyar shirin N-Power ko sauran shirin da ke karkashin tsarin NSIP.
DUBA WANNAN: Biyan bashi: FG za ta rabawa wasu jihohi biyar biliyan N148
"Hankalin ma'aikatar hidimtawa 'yan kasa ya kai kan wani labarin kanzon kurege da ake yadawa a kan cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai sanar da bayar da aiki ga matasan da su ka kamma cin moriyar shirin N-Power a jawabin da zai gabatar ranar 12 ga watan Yuni.
"Ma'aikatarmu na yin kira ga jama'a a kan su yi watsi da wannan sako domin labarin kanzon kurege ne," kamar yadda ma'aikatar ta bayyana a cikin sanarwar.
A kwanakin baya ne ministar ma'aikatar, Sadiya Umar Farouq, ta sanar da cewa za a yaye matasan da aka fara dauka domin samun gurbin daukan wasu sabbi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng