Yadda aka baiwa matan yan majalisa N80m don zuwa Dubai - Kakakin majalisan Ikko, Obasa

Yadda aka baiwa matan yan majalisa N80m don zuwa Dubai - Kakakin majalisan Ikko, Obasa

Kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa ya gurfana gaban kwamitin binciken majalisar da aka shirya domin binciken zargin da ake masa na almindahanan wasu makudan kudade.

Kwamitin mutane tara (9) karkashin jagorancin dan Hanarabul Victor Akande sun saurari bayanansa kan wasu kudade da ake zargin ya kashe.

Za ku tuna cewa SaharaReporters ta saki wasu bayanan cewa kakakin majalisar dokokin na jihar Legas na da asusun banki akalla 60 da yake boye kudin sata.

A gaban kwamitin binciken, Kakakin ya karyata dukkan zarge-zargen da ake masa, inda yayi bayanin cewa babu abinda yayi ba tare da sa hannun majalisar ba, TheCable ta ruwaito.

A martaninsa kan kashe N258m wajen wallafa katin gayyatan bikin rantsar da su bayan nasarar da suka samu a zabe, ya ce babu gaskiya cikin zargin saboda N1.1m kawai aka kashe don yin katin gayyatar.

Yace: "Ba zai yiwu a kashe N258m wajen wallafa katin gayyata ba. Ba ma irin wannan almubazzarancin."

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Yadda aka baiwa matan yan majalisa N80m don zuwa Dubai - Kakakin majalisan Ikko, Obasa
Kakakin majalisan Ikko, Obasa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Bayan samun sabon bulla 2 a Kebbi, Almajirai daga Kaduna sun kai 11 Sokoto

Yayinda aka bukaci bayani kan N80m da aka kashe wajen wani shirin horo a Dubai, Kakakin ya ce iyalan yan majalisa ashirin (20) suka halarci taron.

"Mun baiwa kowacce cikinsu milyan hudu (N4m) na kudin tikitin jirgi, otal, abinci da zirga-zirga."

"Kudin tikitin jirgi kadai milyan biyu (N2m) ne."

"Majalisar dokokin jihar ta wuce yadda kuke tsammani kuma wajibi ne mu horar da mutane kuma kudi ake kashewa a hakan."

"Neman ilimi ba abu bane mai arha kuma kafin yanzu ban taba karban N80m lokaci daya ba."

"Wannan zarge-zargen kawai ana yi ne domin tsige Kakaki daga kujerarsa." A cewarsa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel