Bankin AfDB ta amince da baiwa Najeriya bashin $288.5m

Bankin AfDB ta amince da baiwa Najeriya bashin $288.5m

Kwamitin diraktocin bankin cigaban Afirika AfDB ta amince da taimakawa Najeriya da bashin $288.5m don takaita illar cutar COVID-19 kan tattalin arziki da al'ummar kasar.

A cewar jawabin da ta saki ranar Juma'a, bankin zata karfafa shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi wajen dakile cutar Coronavirus.

Babban diraktar bankin kan Najeriya, Evrima Faal, yace: "Shirin da za'a kaddamar zai tabbatar da cewa an taimaki tattalin arzikin domin iya jure duk irin girgizan da cutar COVID-19 zai haifar."

"Bankin ta kafa hanyoyin SA IDO DA bibiyan yadda za'a kashe wadannan kudaden na COVID-19 tare da tattaunawa na musamman da ofishin Odito Janar na Najeriya domin tabbatar da cewa an yi gaskiya da ayyuka da kudaden,"

Bankin AfDB na cikin bankunan da gwamnatin tarayyar Najeriya ta nemi bashi domin habaka tattalin arzikinta.

KU KARANTA: Jerin jihohin Arewa 3 da suka sallami dukkan masu Koronansu

Bankin AfDB ta amince da baiwa Najeriya bashin $288.5m
Bankin AfDB ta amince da baiwa Najeriya bashin $288.5m
Asali: UGC

Za ku tuna cewa a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2020, Majalisar wakilan tarayya ta amincewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, karban bashin $22.7bn daga kasar waje.

Yan majalisar sun amince da karbo bashin ne a zaman majalisan da ya gudana ranar Talata bayan samun rahoton kwamitin basussuka.

Za ku tuna cewa lokacin da shugaba Buhari ya mika bukatar karban bashin a 2019, ya ce za'ayi amfani da su wajen wasu manyan ayyuka don jin dadin al'umma.

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel