Yadda Sanata ta tube rigarta yayin taro a Intanet

Yadda Sanata ta tube rigarta yayin taro a Intanet

Sanata mace a kasar Mexico mai suna Martha Lucia Micher, ta bada hakurin tube riga da ta yi yayin da suke taron gwamnati ta yanar gizo. Ta yi kokarin canja riga ne bayan ta manta cewa har a lokacin taron bai kare ba.

Martha Lucia Micher Mai shekaru 66 ta manta da cewa kamara kunne take a yayin da ta so sauya riga.

Lamarin ya faru ne lokacin da suke taron jami'an gwamnati a manhajar Zoom, matakin da gwamnatin kasar Mexico ta dauka don dakile yaduwar annobar korona a kasar.

A halin yanzu, Martha Lucia Micher ta mika sakon ban hakurinta a kan kuskuren da ta tafka, ta danganta hakan da rashin ilimin fasahar.

Tube rigar sanata mace yayin taro ta yanar gizo ya jawo cece-kuce
Tube rigar sanata mace yayin taro ta yanar gizo ya jawo cece-kuce. Hoto daga Daily Mail
Asali: UGC

Kamar yadda kafafen yada labarai suka bayyana, a kalla sanatoci 15 ne suka halarci taron tare da gwamnan babban bankin Mexico da wakilan kafafen yada labarai.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wata budaddiyar wasika da ta wallafa a yanar gizo, Micher ta yi bayanin aukuwar lamarin kamar haka:

"A jiya ne wani al'amari ya faru yayin da muke taron sanatoci ta yanar gizo a kan halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki.

"Ba tare da na san kamara na kunne ba a na'urata mai kwakwalwa, na sauya kaya inda na bayyana tsirara.

"Na ci gaba da harkokina amma kiran sanata Alejandro Armenta Mier da Ovidio Peralta Suarez ne suka sa na gane kuskure na."

Sanatar ta ci gaba da mika ban hakurin ta inda ta ce akwai wasu dokoki da bai kamata ko waye ya take ba kuma ta danganta kurenta da rashin isasshen ilimin fasahar.

Tuni hotunan sanatar babu riga ya fara yawo a yanar gizo, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Micher, wacce ita ce shugaban hukumar daidaito ta jinsi, ta yi martani a kan wannan caccakar da sha ta wasikar ta. Ta ce bata jin kunyar yanayin jikinta.

"Ni ce Malu Micher kuma bana jin kunyar yanayin jikina da ya bayyana sakamakon rashin sani.

"Ni mace ce mai shekaru 66 wacce ta shayar da yara hudu. Uku daga cikinsu kwararru ne kuma maza ne da suka san abinda suke yi. Ina alfahari da yanayin jikina.

"Ni mace ce da na kasance a mulki tare da kare hakkin wasu na shekaru 40 kuma na rike mukamai daban-daban. Bana jin kunyar yanayin jikina."

Da yawa daga cikin abokan aikinta sun sake wallafa wasikarta a kafafen sada zumuntar zamani don nuna goyon baya ga sanatar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel