Hukuncin kotun koli: Tubabben hakimi a Kano, Danagundi, ya yi martani mai zafi

Hukuncin kotun koli: Tubabben hakimi a Kano, Danagundi, ya yi martani mai zafi

Tubabben hakimin Gabasawa tun zamanin mulkin Marigayi Ado Bayero, Amin Babba Dan'agundi, ya ce zai ci gaba da addu'a ga Allah da ya bi masa hakkinsa sakamakon zaluntarsa da aka yi.

Tubabben basaraken, ya bayyana hakan ne bayan hukuncin da kotun kolin Najeirya ta yanke bayan shekaru 17 da tube masa rawani.

A tattaunawar da BBC ta yi da basaraken bayan hukuncin kotun kolin, tsohon basaraken ya ce ko da ya so karbar hakkinsa, amma hukuncin Allah ya fi masa.

Ya kara da cewa, bai taba tsammanin rashin nasara ba a karon karshe don kuwa duk kotunan da ya je a baya shi ya yi nasara.

"Na karba wannan hukuncin kuma bani da ja a kai. Amma duk wanda ya ke gani ya taka wata rawar gani, na bar shi da Allah.

"Tun farko hakkina na bukata kuma har yanzu ina nan zan gaya wa Allah ya yi min sakayya," yace.

Tubabben basaraken ya ce ya matukar jin dadin ciresa da aka yi daga sarautar don a halin yanzu Allah ya yi masa suturar da bai masa da ba.

Hukuncin kotun koli: Tubabben hakimi a Kano, Danagundi, ya yi martani mai zafi
Tsohon Sarkin Dawaki Maituta, Alhaji Aminu Dan'agundi. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A jiya Juma'a ne Mai shari'a Mary Odili ta kotun koli ta jagoranci manyan alkalan wajen yanke hukunci.

Hukunci ya jaddada tube rawanin Sarkin Dawaki Maituta kuma hakimin Gabasawa wanda marigayi Ado Bayero ya yi.

A cikin shekarar 2003 ne marigayin basarake, Alhaji Ado Bayerro ya tube rawanin Aminu Babba Dan'agundi daga kujerarsa.

Marigayi Ado Bayero ya zargi hakimin nasa da rashin da'a garesa da aikata wasu laifuka da suka saba da dabi'u nagari.

Daga cikin abubuwan da ake zarginsa da su sun hada da: Shiga harkar siyasa da shirya magudin zabe a 2003, lamarin da ya musanta.

Babu kakkautawa Dan'agundi ya garzaya gaban kotu a Kano inda ya kalubalanci hukuncin sarki da fadar Kano.

Alkali Sadi Mato ya bai wa Dan agundi gaskiya sannan ya bada umarnin mayar masa da rawaninsa tare da biyansa hakkokinsa.

Sai dai kuma, marigayi Ado Bayero ya daukaka kara, wacce a kotun ma Dan'agundi ya sake samun nasarar.

Daga nan kuwa sai sarkin Kano ya sake daukaka kara har zuwa kotun koli, wacce a jiya Juma'a ta aminta da hukuncin marigayin basaraken.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel