Mun sallami karin masu cutar Korona 30 a Abuja - Ministan FCT

Mun sallami karin masu cutar Korona 30 a Abuja - Ministan FCT

Mutane talatin (30) da suka kamu da cutar nan mai toshe numfashi watau COVID-19 a birnin tarayya Abuja sun samu sauki kuma an sallamesu, The Cable ta gano.

Ministan birnin tarayyar, Muhammad Musa Bello, ya bayyana hakan ranar Asabar a shafinsa na Tuwita.

Yanzu adadin wadanda aka sallama a Abuja kawo yanzu ya kai 245.

Yace: "Ya ku mazauna birnin tarayya, na kawo muku labarin farin ciki yayinda muka samu nasarar jinya da sallamar karin masu cutar COVID19 talata (30) daga cibiyoyin killacewarmu."

"Jimillan adadin wadanda aka sallama a FCT yanzu ya kai 245."

Birnin tarayya ce mafi yawan masu cutar COVID-19 a Najeriya bayan jihar Legas da Kano.

Kawo yanzu, Najeriya ta samu mutane 11,844 da suka kamu da cutar Coronavirus. Yayinda 3,696 sun samu sauki kuma an sallamesu, 333 sun rigamu gidan gaskiya, a cewar alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC.

KU KARANTA: Tsohuwa yar shekara 70 ta bayyana yadda matashi yayi mata fyade

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A ranar Juma'a, 5 ga Yuni 2020, hukumar NCDC ta saki rahoton cewa an samu karin mutane 328 da suka kamu da cutar a Najeriya, 70 cikinsu na Abuja.

Yanzu jimillan adadin wadanda suka kamu da cutar a birnin tarayya ya kai 862.

Sauran kadan Abuja ta zarcewa jihar Kano da ke na biyu bayan Legas.

An fara samun karuwar adadin masu cutar a Abuja ne makonni biyu bayan shugaba Buhari ya sassauta dokar kulle da ya sa a Abuja, Legas da Ogun.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun bayyana cewa yanzu da aka kara amincewa a bude wuraren bauta, da yiwuwan adadin ya karu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel