Ban damu da 'tazarce' ba, in ji Gwamna Sule

Ban damu da 'tazarce' ba, in ji Gwamna Sule

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya ce baya damun kansa a kan batun zarcewa a kan mulki karo na biyu a shekarar 2023.

Ya yi wannan furucin ne a hirar da ya yi da manema labarai a Lafiya, babban birnin jiharsa yayin bikin cikarsa shekara daya a kan mulki.

Gwamnan ya yi wa Allah godiya na bashi daman yi wa jiharsa hidima na shekaru hudu wadda ya ce ta isa ya bawa jihar gudunmawa don ciyar ta ita gaba.

Da ya ke amsa tambayar da aka masa a kan yiwuwar mutanen jihar su sake zabensa a 2023, ya ce a shirye ya ke ya koma Amurka ko Saudiyya ya more rayuwarsa bayan waadinsa na shekara hudu ya kare.

Ban damu da 'tazarce' ba, in ji Gwamna Sule
Ban damu da 'tazarce' ba, in ji Gwamna Sule. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A cewarsa, "Zarcewa kan mulki a matsayin gwamna bai taba tayar min da hankali ba. Bari in fada maka, a 1998, lokacin ina aiki a Amurka, na ji aikin ya gundure ni. Na yi ritaya na karbi kudade na na kafa karamin kamfani da muke kula da abinmu.

"Tsamani na shike nan, ban taba tunanin zan dawo Najeriya da zama ba balantana zama shugaban MD African Petroleum da kuma Babban Manaja a Kamfanin Dangote.

"Tun a lokacin na fara jin dadin rayuwa, ba yanzu bane.

"Duk wadandan abubuwan sun faru a rayuwa ta duk da cewa ban san za su faru ba. Allah ne kawai ya saka min albarka har na kawo yau.

"Kwatsam gashi na zama gwamna, yanzu ni gwamna ne kuma wani yana maganan waadi daya, kuma ana tunanin zanyi kuka, inyi barci in mutu? Ba zai yi wu ba!

"Waadi daya ya ishe ni. Haka na ke kallon lamarin. Waadi daya ya wadatar.

"Allah na gode maka da ka bani wa'adi daya.

"Abin bai taba damu na ba kuma ba zai dame ni ba. Har cikin zuciya na haka na ke ji.

"Idan nayi wa'adi daya, walahi talahi, walahi talahi, zan tafi Amurka ko Saudiyya inyi rayuwa ta hankali kwance. Na san EFCC ba za su neme ni ba don bana satan kudin gwamnati.

"Idan anyi wa'adi daya sai mene?

"Bari in fada maka, ina farin ciki da hakan, saboda haka ba zan hana idanu na barci ba don wani ya ce wa'adi daya zan yi.

"Ban taba damuwa ba kuma bana tunanin zan damu," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel