An kama fasinjoji 91 gwamutse da akuyoyi a mota za su shiga Kaduna

An kama fasinjoji 91 gwamutse da akuyoyi a mota za su shiga Kaduna

'Yan sanda da ke jihar Kaduna suna kama wata motar dako dauke da fasinjoji 91, akuyoyi 24, babura 14 a Rigasa da ke karamar hukumar Igabi na jihar.

The unch ta ruwaito cewa babban motar kirar Iveco mai lamba DDM 167 AX ta taso daga Zaria ne za ta nufi Legas.

Rundunar yan sandan ta ce motar ta saba dokar hana zirga zirga da aka saka a jihar domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

An kama fasinjoji 91 gwamutse da akuyoyi a mota za su shiga Kaduna
An kama fasinjoji 91 gwamutse da akuyoyi a mota za su shiga Kaduna. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Jumaa, Mai magana da yawun rundunar, Mohammed Jalige ya ce an kama direba da fasinjojin motar kuma suna tsare.

Jalige ya ce rundunar ta fara bincike a kan lamarin da niyyar gurfanar da wadanda ake zargi kamar yadda dokar hana fita na jihar ta tanada.

Sanarwar ta ce, "Direban motar dakon ya saba dokar hana zirga zirga na kayan da ba na amfanin dole ba inda ya boye fasinjoji 91, akuyoyi 24, babura 14 da wasu buhunna 30 da aka cika da mabanbantan abubuwa.

"An ceto fasinjojin kuma an fara gudanar da bincike a kan lamarin da niyyar gurfanar da su gaban kotu kamar yadda dokar hana fita ta Kaduna ta tanada."

A wani rahoton, kun ji cewa Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wata budurwa mai shekaru 17 mai suna Seun Adekunle tare da saurayinta mai suna Basit Olasunkanmi.

An kama su ne sakamakon zarginsu da ake da hadin baki wajen garkuwa da budurwar.

Wannan na kunshe a wata takarda da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya bai wa manema labarai a Abeokuta.

Oyeyemi ya ce, "An kama su biyun bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar mai suna Bukky Adekunle ta kai wa 'yan sandan Enugada har ofishinsu.

"Ta kai rahoton ne a ranar Alhamis a kan cewa ta aika budurwar kasuwa da ke Abeokuta a ranar 1 ga watan Yunin 2020 amma bata dawo ba."

Ta kara da cewa "Ta samu kiran wani bayan kwanaki biyu inda aka yi ikirarin cewa an yi garkuwa da ita kuma ana bukatar kudin fansa har naira dubu dari biyar idan tana son ganin diyarta a raye."

Mahaifiyar ta ce, "Mai kiran ya kara da jan kunnenta da kada ta kuskura ta kai rahoto wurin 'yan sanda matukar tana fatan ganin diyarta a raye."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel