Mace-macen Kano: Kashi 50 zuwa 60 na da alaka da korona - Ehanire

Mace-macen Kano: Kashi 50 zuwa 60 na da alaka da korona - Ehanire

A kalla kashi 60 daga cikin mace-macen jihar Kano na da alaka da annobar korona, jami'ai suka sanar.

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana hakan a yayin bayanin inda aka kwana a gaban kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa a ranar Litinin.

Jihar yankin arewa maso yamman ta fuskanci yawaitar mace-mace a jihar, kusan rayuka 979 da suka hada da na manyan sarakuna, ma'aikatan lafiya da manyan malamai.

Kamar yadda ministan yace, kashi 50 zuwa 60 na mace-macen na da alaka da cutar korona. Hakan yana nufin 490 zuwa 587 na mutanen da sukar rasu an gano cutar coronavirus ce ta kashesu.

Binciken farko ya bayyana cewa, wasu daga cikin mamatan sun rasa rayukansu ne sakamakon cutar zazzabin cizon sauro ko sankarau, gwamnatin jihar ta sanar.

Wasu daga cikin mace-macen sun auku a jihohin Jigawa da Bauchi inda mutum 150 suka rasu.

Ehanire ya ce har yanzu ana bincike don gano dalilin mace-macen a sauran jihohin.

A ranar 7 ga watan Afirilu, an tabbatar da kamuwar mutum 999 daga cikin 12,486 na masu korona a Najeriya duk a jihar Kano.

Mace-macen Kano: Kashi 50 zuwa 60 na da alaka da korona - Ehanire
Mace-macen Kano: Kashi 50 zuwa 60 na da alaka da korona - Ehanire. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya ce tawagar ministan ce ta gano hakan bayan dogon binciken da ta yi a jihar Kano da goyon bayan kungiyar yaki da cutar ta jihar.

Ya ce an samu mace-macen a kananan hukumomi takwas da ke tsakiyar birnin Dabo a cikin kankanin lokaci.

"Dangane da mace-macen jihar Kano da ya auku a makonni biyar da suka gabata, tawagar ta tabbatar da rasa rayuka 976 a kananan hukumomi takwas daga cikin 44 da ke jihar Kano.

"An kai kololuwa ne a mako na biyu na watan Afirilu. Zuwa farkon watan Mayu, mace-macen ya mtukar raguwa.

"Binciken da aka yi ya bayyana cewa kashi 56 na daga mace-macen duk sun auku a asibitoci.

"Bincike ya nuna cewa, kashi 50 zuwa 60 na mace-macen da suka faru, annobar korona ce ta assasa shi," yace.

Ya kara da cewa, da yawa daga cikin wadanda suka rasu suna da shekaru 65 zuwa sama ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel