Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan bindiga 70 a Kaduna

Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan bindiga 70 a Kaduna

Dakarun Sojin Najeriya tare da gudunmuwar mayakan sama sun ragargaji yan bindigan da suka addabi al'ummar jihar Kaduna a dajin Kachia ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni, 2020.

Kakakin hedkwatan tsaron tarayya, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana cikin jawabin da ya saki cewa Sojin sun kashe akalla yan bindiga saba'in (70) a harin.

Sojojin sun fitittikesu daga garin Gidan Maikeri zuwa dajin dake karamar hukumar Kachia.

Jawabin yace: "A wani harin hadakan sojin kasa da na sama da aka kai ranar 5 ga Yuni, 2020, dakarun sojin Operation THUNDER STRIKE tare da Sojin 312 Atilari da yan banga sun yi sintirin dajin Kachia kuma sun kashe wasu yan bindiga da barayin shanu."

"Hakan ya biyo bayan rahoton da aka samu na ganin wucewan yan bindigan a wajen. Dakarun sun fitittikesu daga garin Gidan Maikeri dake karamar hukumar Chikun zuwa dajin dake karamar hukumar Kachia."

KU KARANTA: Bayan Buhari ya zabeta, Kasar Misra ta bukaci a soke takarar Okonjo Iweala na kujerar WTO

"An gano inda suke kuma jirgi mai saukar angulun ya ragargajesu. Bayan harin saman, an tabbatar da kisan saba'in (70) cikinsu yayinda sauran suka tsira da raunuka."

Saboda haka, muna kira da jama'an dake zaune a wuraren nan su bayyanawa jami'an tsaro duk wanda suka gani da wani raunin da basu yadda ya shi ba. Hakan zai taimaka wajen damke wadanda suka tsira."

"Hakazalika, dakarun sojin Operation YAKI sun damke masu taimakawa yan bindigan da kayayyaki a wajen kauyan Kankomi."

"Abubuwan da aka samu a hannunsu sun hada da katin waya, sigari, lemun kwalba da kayan masarufi."

Hedkwatar tsaron ta jinjinawa dakarun bisa gagarumin nasarar da suka samu kuma tayi kira ga jama'an gari su baiwa jami'an tsaron rahotannin da zai taimaka wajen kawar da yan ta'addan.

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumI

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel