Gasar tikar rawa a gaban miji ta jawo cece-kuce a arewacin Najeriya

Gasar tikar rawa a gaban miji ta jawo cece-kuce a arewacin Najeriya

A ranar 25 ga watan Mayu ne aka sha shagalin sallah. A ranar kuwa aka dinga ganin bidiyon matan aure na tikar rawa a gaban mazansu.

Al'amarin ya fara ne bayan Aisha Falke, mamallakiyar shafin Northern Hibiscus a Instagram ta ga wata mata ta cashe rawa a gaban mijinta.

Gasar mai suna #danceforhusband ta yadu a kafafen sada zumuntar zamani sannan ta matukar jawo cece-kuce daga jama'a.

Masu tsokaci suna cewa wannan ba al'adar matan arewa ba ce don an san su da kunya tare da rufe sirrin aure.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, an bukaci masu gasar da su kwashi rawa a katon falo mai cike da kayan alatu. Dole ne matar ta saka rigar leshi doguwa tare da awarwaro a hannayenta.

Dole ne mijinki ya kasance a zaune a falon yayin da wakar Jarumar mata wacce mawaki Hamisu Breaker ya rera ta dinga tashi.

Jaridar Daily Trust ta yi kokarin jin ta bakin mawaki Hamisu Breaker, amma al'amarin ya gagara don lambar wayarsa bata tafiya.

A yayin martani a kan wannan ci gaba, jarumar Kannywood, Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso, ta wallafa wasu daga cikin bidiyon a shafinta na Instagram inda take cewa: "A wannan sallar mun ga soyayya a zahiri. Me kuke tunani? In wallafa nawa bidiyon ne ko kuwa?"

Gasar tikar rawa a gaban miji ta jawo cece-kuce a arewacin Najeriya
Gasar tikar rawa a gaban miji ta jawo cece-kuce a arewacin Najeriya. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Jarumi Abba El-Mustapha ya ce, "Idan mace bata saba nuna irin wannan soyayyar ga miji ba, akwai yuwuwar ta rasa shi."

A wani bidiyo na daban, Mansurah ta yi tsokaci inda ta ce, "Wannan mutumin daga gani ya saba halartar biki. Yadda yake yi mata liki da kudi kadai ya bayyana."

Amma kuma, wani fitaccen ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya ce daya daga cikin tsoffin iyayen gidansa ya saki matarsa bayan wallafa irin wannan bidiyon da ta yi.

Ya ce, "Daga Allah muke, gareshi za mu koma. Yanzu nake samun labarin cewa wani tsohon ubangidan ya saki matarsa a kan sakin bidiyon da ta yi na gasar rawar nan a daren jiya.

"Wannan abun takaici ne yadda auren shekaru 19 da yara 3 ya zo karshe. Ita ce kadai matarsa."

Babban editan jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar ya rubuta, "Duk da ban dauka wannan al'amari da muhimmanci ba, shiyasa nake ganin bai dace ba."

Tsokaci sun ci gaba da zuwa kala-kala inda wasu ke goyon bayan matan yayin da wasu ke sukarsu a kan wannan sabuwar dabi'ar.

A yayin martani game da wannan ci gaba, Aisha Falke ta ce: "Muna damuwa sosai a kan abubuwan da basu shafemu ba a rayuwa.

"Me ye abun damuwa a kan wannan al'amarin bayan ana yi wa yaranmu kanana fyade? Ana yaudarar 'yanmatanmu a kan cewa za a auresu? Auren kananan mata yana tsinkewa a kowacce rana?"

A wani bidiyo da ta wallafa, Falke ta ce ba ita ta fito da wannan gasar ba kuma zancen sakin da aka ce an yi duk na bogi ne babu gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel