Kano: An kama maganin 'kara karfin maza' na Naira miliyan 25

Kano: An kama maganin 'kara karfin maza' na Naira miliyan 25

Hukumar lura da zirga zirgan ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta kama mota makil da kayan kara karfin maza da kudinsa ya kai Naira miliyan 25 a unguwar Sabon Gari na jihar.

A sanarwar da ya fitar ranar Asabar, Kakakin KAROTA, Nabilusi Kofar Naisa ya ce an gano kwayar mai suna Arofranil ne sakamakon wasu bayyanan sirri da ya nuna magungunan ba su da lambar NAFDAC.

A cewarsa, an kama maganin da ake zargin jabu ne a New Road park, Sabon gari cike makil a mota kafin a raba wa shugabannin kasuwanni.

Kano: An kama mota dauke da maganin karfin maza na N25m
Kano: An kama mota dauke da maganin karfin maza na N25m. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

Kakakin ya kara da cewa masu maganin sun tsere sun bar shi a lokacin da aka kai sumamen inda ya ce ana kokarin kamo su.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Sanarwar ta ce, "A kalla sinkin magungunan 5000 ne jami'an karota suka kama yayinda har yanzu ana kokarin kama masu maganin domin sun tsere lokacin da aka kai sumamen."

Mai magana da yawun KAROTA ya cigaba da cewa za su mika magungunan da hukumar Lafiya ta jihar domin daukan matakin da ya dace kamar dai yadda suka saba.

Shugaban hukumar Dr. Baffa Babba Dan’agundi ya yi kira ga alumma su cigaba da basu goyon baya da hadin kai domin su cigaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata.

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya sanar da cewa a baya gwamnatinsa ta dau nauyin a kalla yaran Fulani makiyaya 74 zuwa Turkiyya don koyo yadda ake tatso madara na zamani.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin kaddamar da rukunin gidaje 200 na Ruga sa za a gina wa Fulani a kauyen Dansoshiya da ke karamar hukumar Kiru ta jihar.

Ya kara da cewa, gwamnatinsa ta samar da tafkin dan Adam mai cin ruwa lita miliyan hudu don amfanin Shanun Fulanin wanda hakan zai sa rashin bukatar yawon neman ruwansu.

Kamar yadda yace, ana gayyatar Fulani makiyaya daga dukkan sassan kasar nan sa su garzaya jihar Kano son mora daga romon gwamnatinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel