COVID-19: Karin mutum 328 sun harbu a Najeriya, jimilla 11844

COVID-19: Karin mutum 328 sun harbu a Najeriya, jimilla 11844

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 328 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.42 na daren ranar Juma'a 5 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 328 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-121

FCT-70

Bauchi-25

Rivers-18

Oyo-16

Kaduna-15

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Gombe-14

Edo-13

Ogun-13

Jigawa-8

Enugu-6

Kano-5

Osun-2

Ondo-2

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Juma'a 5 ga Yuni 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 11844.

An sallami mutum 3696 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 333.

A wani labarin kunji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta saka almajirai 1,322 makarantu bayan an dawo mata da su jihar sakamakon barkewar annobar korona a jihohin kasar nan.

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a kan annobar korona a ranar Laraba a garin Dutse.

"Kamar yadda na bayyana a jawabi na na baya, an dawowa jihar Jigawa da almajirai 1,322 daga jihohi daban-daban. Mun kula da su kuma muna samar musu da kayayyakin more rayuwa.

"Mun mika dukkan almajiran hannun iyayensu banda 23 daga ciki da ke dauke da cutar coronavirus amma suna karbar magani a cibiyar killacewa.

"Mun bada umarnin saka yaran a makarantar firamare tare da ci gaba da basu ilimin Qur'ani," in ji Badaru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel