Labari da dumi: Mamban kwamitin yaki da korona ya rasu

Labari da dumi: Mamban kwamitin yaki da korona ya rasu

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya sanar da mutuwar Remi Omotoso, daya daga cikin mambobin kwamitin yaki da cutar korona kuma tsohon shugaban Standard Chartered Bank.

A wata takardar da Yinka Oyebode, sakataren yada labarai na Fayemi ya fitar, ya ce Omotoso ya rasu a ranar Juma'a bayan gajeriyar rashin lafiya.

Ya rasu yana da shekaru 75 cif a duniya.

Ya kwatanta marigayi Omotoso, wanda dan asalin Ayedun-Ekiti, a matsayin da nagari ga jihar Ekiti kuma kwararren masani a fannin kudi.

Kamar yadda yace, "Duk da ayyukan da suke sha wa Omotoso kai, yana zuba lokacinsa, kudinsa da karfinsa wajen gyara rayuwar jama'a.

"A koda yaushe, shirye yake ya bada goyon baya don samun mulki nagari. Yana hakan ne cike da gogewarsa da kuma kwarewar da ya samu," gwamnan yace.

"Garemu wannan babbar rashi ne. Remi Omotoso daya ne tamkar dubu. Ya wakilci jihar Ekiti sannan ya nuna bajintarsa. Har gobe muna alfahari da shi kuma madubin dubawa ne ga na baya.

"Duk da rashin fasaharsa da muka yi, muna farin cikin irin rayuwar da yayi tare da tarihin da ya kafa. Zai kasance abun alfaharinmu."

Kafin mutuwarsa, a ranar 4 ga watan Afirilun 2020, Fayemi ya nada shi mamba a kwamitin yaki da cutar korona.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, shugaban kwamitin yaki da annobar korona ta jihar Kano, Dr Tijjani Hussein, ya bayyana cewa makonni kadan suka rage cutar ta yi kaura daga jihar Kano.

Hussein, wanda ya bayyana hakan a yayin tattaunawa a kan inda aka kwana a kan cutar a jihar Kano a ranar Alhamis, ya yi kira ga mazauna jihar da su dauka matakan dakile yaduwar cutar.

Ya ce: "Idan mazauna jihar Kano za su kiyaye dokokin wanke hannu, saka takunkumin fuska da kuma nesa-nesa da juna, ina tabbatar da cewa nan da makonni kalilan za a nemi korona a Kano a rasa."

Shugaban kwamitin ya kara da cewa, dukkan masu cutar da aka samu an samo su ne daga kananan hukumomi 30 na jihar amma kuma kashi 90% daga cikin masu cutar 'yan birnin Kano ne.

Ya kara da cewa, kashi 76 na masu cutar a jihar maza ne inda kashi 24 suka kasance mata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel