'Yan bindigan da suka kashe mutum 70 a Sokoto Fulani ne - Gobir

'Yan bindigan da suka kashe mutum 70 a Sokoto Fulani ne - Gobir

Mashawarci na musamman ga Ministan Harkokin 'Yan Sanda kuma tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, Idris Gobir ya yi magana a kan harin da aka kai Sabon Birni inda aka kashe mutum 70.

Gobir ya yi hira ta musamman ne da Adeniyi Olugbemi inda suka tattauna a kan lamarin tsaro a jihar Sokoto da wasu batutuwan kamar yadda The Punch ta wallafa.

A cewar Gobir, Fulani ne suka kai harin, "amma ba makiyaya ba wadanda ke kiwon dabobi, wadannan bata gari ne daga cikinsu. Akwai alamu sosai da ke nuna yan bindigan da ke adabar mu Fulani ne.

'Yan bindigan da suka kashe mutum 70 a Sokoto Fulani ne - Gobir
'Yan bindigan da suka kashe mutum 70 a Sokoto Fulani ne - Gobir. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Za ka iya gane su ta siffansu da harshensu, ko a lokacin da ake tattaunawa da su don biyan kudin fansa, harshen Fulfulde suke magana da shi.

"Idan sun kawo hari, ba su raga wa kowa har Fulani 'yan uwansu, suna kashe Fulani, suyi garkuwa da su ko suyi musu fashi. Kowa ya sansu kuma mutane sun san inda suke zaune."

Har wa yau, ya ce 'yan bindigan sun nemi taimako daga wasu bata gari irinsu daga Isa/Bafarawa a jihar Sokoto da kuma wasu da ke Maradun a karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara kafin kai harin.

Ya cigaba da cewa mutanen gari suna taka rawar da ya dace wurin taiamakawa hukumomin tsaro da bayanai masu amfani amma wasu lokutan yan bindigan sukan kai harin ramuwar gayya ga al'umma da ke tseguntawa hukumomin tsaro.

"Wasu lokutan babu yadda mutane za suyi da su domin fada da yan bindiga ba abu ne mai sauki ba. Kangararru ne da suka kwashe shekaru masu yawa suna zaune a daji.

"Sun fi jami'an tsaron sanin yadda dajin ya ke. Kai musu farmaki a mabuyansu yana da wahala, kaman sojoji ne su tafi yaki da masu satar man fetur a cikin ruwa," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel