Da duminsa: Bayan Buhari ya zabeta, Kasar Misra ta bukaci a soke takarar Okonjo Iweala na kujerar WTO

Da duminsa: Bayan Buhari ya zabeta, Kasar Misra ta bukaci a soke takarar Okonjo Iweala na kujerar WTO

- Ofishin Jakadancin Misra ta soki zaben Okonjo Iweala da Buhari yayi

- An zargi shugaba Buhari da yin abu sabanin hukuncin da gammayar AU ta yanke

- Shugaban kasar Misra, AbdelFatah El-Sisi ne shugaban gamayyar kasashen Afrika AU

Kasar Misra ta bukaci a soke takarar Ngozi Okonjo-Iweala na kujerar shugabar kungiyar kasuwancin duniya W.T.O kwana daya bayan Buhari ya zabeta ta wakilci Najeriya, The Cable ta samu labari.

Ta ce tun watanni biyar da suka wuce, 30 ga watan Nuwamba, 2019, aka bukaci kasashe su aika sunayen yan takarar kujerar amma sai yanzu Buhari ya kawo sabon suna.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoto ranar Alhamis cewa shugaba Muhammadu Buhari ya janye takarar Yonov Frederick Agah, kuma maye shi da Ngozi Okonjo Iweala matsayin wacce za tayi takarar kujerar shugabar WTO.

Da duminsa: Bayan Buhari ya zabeta, Kasar Misra ta bukaci a soke takarar Okonjo Iweala na kujerar WTO
Okonjo Iweala na kujerar WTO
Asali: UGC

KU KARANTA: An damke wani mutum yana kokarin luwadi da mara lafiya (Bidiyo)

A wasikar da kasar Misra ta tura, jakadan kasar zuwa gamayyar kasashen Afrika AU ya ce kundin dokoki ya nuna cewa zaben sabon dan takarar da Najeriya tayi "ya sabawa hukuncin da majalisar zartarwa ta yanke."

A wasikar mai ranar wata 5 ga Yuni, 2020 da The Cable ta samu, ofishin jakadancin kasar Misran ta bukaci kwamitin zaben yan takara ta sanar da wakilar nahiyar Afirka dake Geneva, kasar Swizalan cewa Abdulhameed Mamdouh na Misra da Eloi Laourou na kasar Benin "kadai ne yan takaran Afrika da aka tabbatar”.

Ofishin jakadancin ta bukaci ofishin lauyoyin gamayyar kasashen Afrika AU ta tofa albarkacin bakinta kan hallacin canjin da Najeriya tayi dubi da hukuncin majalisar zartarwa na EX1072 na Yulin 2019, da ta bukaci kasashe su gabatar da sunayen yan takararsu zuwa ranar 30 ga Nuwamba, 2019.

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Okonjo Iweala, ta rike kujeran ministar kudin Najeriya daga shekarar 2003 zuwa 2006 karkashin shugaba Olusegun Obasanjo da kuma a shekarar 2011 zuwa 2015 karkashin Goodluck Jonathan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng