Bayan shekaru shida da rasuwar Sarki Ado Bayero, an yi taron addu'a a fadar masarautar Kano

Bayan shekaru shida da rasuwar Sarki Ado Bayero, an yi taron addu'a a fadar masarautar Kano

Fadar masauratar Kano ta cika makil yayin da aka yi taro na musamman domin gudanar da addu'o'i shekaru shida bayan rasuwar tsohon Sarki, Ado Abdullahi Bayero.

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero sun halarci taron a fadar da ke cikin karamar Hukumar birni wato Kano Municipal.

Limamin Kano Farfesa Sani Zahraddin, shi ne ya jagoranci addu'o'in tare da sauran manyan malamai na jihar Kano.

Hakimai da dama sun halarci taron kamar yadda hotunan da hadimin gwamna Ganduje a kan sabuwar hanyar sadarwa, Salihu Tanko Yakasai, suka bayar da shaida.

KARANTA KUMA: Kungiyar NAAC ta nemi Buhari ya sauke shugabannin tsaro domin ceto Najeriya

Ado Abdullahi Bayero ya rayu daga ranar 25 ga watan Yulin shekara 1930 zuwa 6 ga watan Yunin 2014, inda mai yankan kauna ta cimma masa bayan ya sha fama da jinya.

An nada shi sarki a ranar 13 ga watan Oktoba na 1963, kuma tabbas tarihin jihar ba zai cika ba muddin babu na Marigayi Sarki Ado a cikinsa.

Shi ne tsohon sarkin Kano tun daga shekarar 1963 har zuwa rasuwarsa a 2014. Ya shafe shekaru 51 a kan karagar mulki.

Ya bar duniya yana da shekara 84. Margayi Alhaji Ado Bayero, shi ne basaraken da ya fi kowanne dadewa a kan mulki a tarihin Masarautar Kano.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Bayero kafin ya zama sarkin Kano, ya kasance shahararren dan kasuwa, kuma yayi aikin banki a Bank of British West Africa har zuwa shekarar 1949.

Ya kasance tsohon jami'in dan sanda wanda kuma ya yi aiki a matsayin jakadan Najeriya a Kasar Senegal.

Danginsa na Sullubawan Fulani, su ne ke rike da masarautar Kano tun daga shekarar 1819. Mahaifinsa shi ne Abdullahi Bayero da kuma mahaifiya, Hajiya Hasiya.

Shi ne na goma sha daya a jerin 'ya'yan da mahaifinsa ya haifa, kuma shi ne na biyu a wurin mahifiyarsa.

Mahaifinsa ya mulki masarautar a tsawon shekaru 27, inda kuma dan uwansa, Muhammadu Sanusi na farko, ya gaji sarautar daga shekarar 1953 zuwa 1963.

Bayan tsige Sarki Sanusi na farko a shekarar 1963, Muhammadu Inuwa ya haye gadon mulki inda ya shafe wata uku kacal sai ajali ya katse masa hanzari.

Sarki ya karbi ragamar fadar masarautar Kano bayan rasuwar Muhammadu Inuwa. Ya kasance Sarki na 56 a tarihin masauratar.

Kuma shi ne Sarki na 13 a tarihin Sarautar Fulani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel