Masarautar Kano: Kotun koli ta jaddada tube wa Danagundi rawani

Masarautar Kano: Kotun koli ta jaddada tube wa Danagundi rawani

Kotun koli ta jaddada tube rawanin tsohon Sarkin Dawaki Maituta kuma hakimin Gabasawa, Alhaji Aminu Babba Danagundi.

Marigayi tsohon sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ne ya tube rawanin hakimin Gabasawa kuma Sarkin Dawaki Maituta a shekarar 2003.

A lokacin da tubabben hakimin ya yi nasarar a kotun a kan sarkin, an zargi hakimin da kin biyayya ga marigayin sarkin wanda ya gayyaci hakimin amma ya ki zuwa.

A yayin yanke hukunci a ranar Juma'a, kotun kolin karkashin shugabancin Jastis Mary Odili, ta jaddada hukuncin kotun daukaka kara.

Masarautar Dabo ta daukaka kara a kan hukuncin kotun daukaka kara a Kano, wanda ya aminta da hukuncin babbar kotun jihar a kan hana tube rawanin Danagundi.

Idan za mu tuna, babu jimawa da tube rawanin Danagundi, ya maka marigayi Ado Bayero da masarautar Kano a gaban kotu.

Da farko, Jastis Saka Yusuf ya fara shari'ar amma daga baya sai aka koma wata kotu a karkashin jagorancin Jastis Sadi Mato.

Jastis Mato ya yanke hukuncin cewa a mayar wa da Danagundi rawaninsa sannan a biya sa dukkan abinda ya dace.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Marigayi Alhaji Ado Bayero ya nada Alhaji Aminu Babba Danagundi a matsayin Sarkin Dawaki Maituta kuma hakimin Gabasawa a shekarar 1999.

Danagundi ya kwashe shekara 13 a kan karagar mulkin kafin al'amari tsakaninsa da marigayin sarki ya rincabe har ya tube masa rawani.

An maye gurbinsa da Sarkin Dawaki Maituta na yanzu, Alhaji Bello Tuta.

A yayin zantawa da jardar Daily Trust ta wayar tarho, Danagundi ya ce yana da tabbacin kotun koli za ta yi adalci a kan shari'ar.

Ya ce: "Zan yi matukar farin ciki idan na koma matsayina na Sarkin Dawaki kuma hakimin Gabasawa idan kotu ta amince a mayar da ni.

"Wannan al'amari ne da na dinga bibiya na tsawon shekaru 17. A shirye nake in koma kujerata.

"Wannan abu ne da na dinga jira na tsawon shekara 17. Don haka ne nake jiran hukuncin kotun koli mai cike da adalci."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel