Matawalle ya rantsar da sabbin kantomomi 14 a jihar Zamfara

Matawalle ya rantsar da sabbin kantomomi 14 a jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya yi nadi tare da rantsar da sabbin kantomomi na kananan hukumomi 14 da ke jihar.

Ana iya tuna cewa, a zaman majalisar dokokin jihar karo na biyu da aka tsawaita shi zuwa ranar Alhamis, an sauke dukkanin shugabannin kananan hukomomi 14 na jihar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, majalisar ta yanke wannan hukunci ne saboda tabargazar kudi da wulakantar da kujera da shugabannin kananan hukumomin suka yi.

Gwamna Matawalle cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Zailana Bappa ya gabatar, ya ce an yi sabbin nade-naden kwana daya kacal da sauke shugabannin kananan hukumomin.

Gwamna Muhammadu Bello Matawalle na jihar Zamfara
Gwamna Muhammadu Bello Matawalle na jihar Zamfara
Asali: UGC

Mallam Bappah ya ce gwamnan bai yi wata-wata ba wajen daukan shawarar da majalisar dokokin jihar ta bayar a fafutukar da gwamnatinsa ta ke yi na kare martabar al'ummar jihar.

Ya yi kira ga sabbin kantomomin da su jajirce wajen yin bitar da nazari sha'anin tsaro da ya addabi jihar. Ya bukaci su kawo masa rahoton tsaro na kowace karamar hukuma nan da mako biyu.

KARANTA KUMA: Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu

Haka kuma, Gwamna Matawalle ya rantsar da sabon kwamishinan Ma'aikatar Kimiya da Fasaha da ya nada da kuma wasu Sakatarori na dindindin guda uku.

Jerin kantomomin da aka rantsar tare da kananan hukumomin da za su wakilta sun hadar da;

Ahmed Balarabe (Anka)

Abu Makau (Bakura)

Muhammad Umar (Birnin Magaji)

Nasiru Zarumi Masama (Bukkuyum)

Abdulazeez Ahmed (Bungudu)

Ibrahim D Ibrahim (Gummi)

Sanusi Sarki (Gusau)

Salisu Isah Dangulbi (Maru)

Shehu Muhammad Faru (Maradun)

Lawali Isah Abdullahi (Kauran Namoda)

Sani Galadima (Shinkafi) da kuma

Abubakar Musa (Talata-Mafara).

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Sabon kwamishinan Ma'aikatar Kimiya da Fasaha da aka rantsar shi ne, Lawal Abubakar.

Sai kuma sabbin sakatarorin dindindin da suka hadar da:

Abubakar Jafar Maradun (Ofishin Gwamna)

Garba Ahmad Gusau (Ma'aikatar Kudi) da kuma

Bala Umar (Ma'aikatar Kasa).

A bangare daya kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan kimanin makonni goma da rufe dukkan Masallatai da majam'iu a fadin kasar, shugaba Muhammadu Buhari ya halarci Sallar Juma'a a yau 5 ga watan yuni, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel