Yanzu-yanzu: Babu cutar korona a jihar Kogi, na dage dokar kulle - Yahaya Bello
- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya sanar da dage dokar hana zirga-zirga da ya saka wa karamar hukumar Kabba-Bunu
- Gwamna Bello ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a, 5 ga watan Yunin 2020 a gidan gwamnatin jihar da ke Lokoja
- Duk da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta ce akwai cutar a jihar, gwamnan ya musanta hakan
Gwamnatin jihar Kogi ta dage dokar hana zirga-zirga da ta saka a karamar hukumar Kabba-Bunu ta jihar bayan an zargi yaduwar annobar korona.
Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi, ya sanar da hakan ne a yau Juma'a a gidan gwamnati da ke Lokoja, babban birnin jihar.
Ya ce dole ce ta sa aka dage dokar don dukkan samfur din jini da aka dauka a karamar hukumar sakamako ya nuna basu dauke da cutar, jaridar The Cable ta wallafa.
Gwamnan ya sake jaddada cewa babu cutar korona a jiharsa duk da ikirarin hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta ce an samu karin mutum uku masu cutar.
Karin bayani na tafe...

Asali: Twitter
KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng