Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu

Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu

- Daga karshe Sanata Orji Kalu ya dawo gida bayan an sako shi daga Kurkukun Kuje

- Shugaban Majalisar Dattawa ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Sanatan a gidansa na Abuja

- Kotun kolin ta warware hukuncin daurin shekaru 12 da aka yiwa Sanata Kalu kan laifin almundahana N7.65b

Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu
Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu
Asali: Facebook

KARANTA KUMA: 'Yan Boko Haram sun ci gaba da mika wuya yayin da Sojoji ke musu kisan kare dangi - DHQ

Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu
Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu
Asali: Facebook

Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu
Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu
Asali: Facebook

Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu
Ahmed Lawan ya jagoranci tawagar Sanatoci zuwa gidan Orji Kalu
Asali: Facebook

A Yammacin ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya jagoraci tawagar wasu sanatoci da suka kai ziyara har gidan Orji Uzor Kalu.

Legit.ng ta lura cewa, tawagar manyan sanatocin ta ziyarci Uzor Kalu, bulaliyar masu rinjaye a majalisar dattawa, biyo bayan sakinsa daga gidan kurkuku a ranar Laraba, 3 ga watan Yuni.

Sanata Kalu da 'yan majalisar da suka kai masa ziyara sun sanya takunkumin rufe fuska, sai dai ba su kiyaye dokar nesa-nesa da bayar da tazara a tsakanin juna ba.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

An sallamo tsohon gwamnan jihar Abia daga gidan gyara hali na Kuje bayan ya shafe tsawon watanni yana cin sarka. Ya kuma koma gidansa na Abuja.

A watan Dasumba na shekarar 2019 ne aka yankewa Kalu hukuncin dauri na shekaru 12, sanadiyar laifin almundahana ta naira biliyan 7.65 da ya aikata yayin da ya ke gwamna.

Sai dai Kotun Kolin kasar ta soke wannan hukunci inda ta ba da umarni a sake masa sabuwar shari'a.

Kotun Kolin, wacce ta soke hukuncin yayin bayar da dalili ta bayyana cewa, alkalin da ya yanke hukuncin ba shi da hurumin yi wa tsohon gwamnan shari'a.

Ta na mai cewa, "Mai Shari'a Mohammed Idris na kotun tarayya ta Legas da ya yanke hukuncin, an riga an daga likafarsa zuwa matsayin alkalin Kotun Daukaka Kara ta kasar, don haka ba shi da hurumin yanke hukunci kan shari'ar Mr Kalu."

Legit.ng Hausa ta kuma ruwaito cewa, masu zanga-zanga a karkashin kungiyar al'umma masu kishi reshen jihar Abiya ta Arewa, a ranar Talata sun mamaye majalisar dokoki ta tarayya.

Sun yi kira ga shugaban majalisar dattawa, da ya yi gaggawar sanya kujerar Sanata Orji Uzor Kalu a kasuwa.

A cewar kungiyar, sanya kujerar a kasuwa zai sa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gudanar da sabon zabe domin samar da wanda zai wakilci Abia ta Arewa a Majalisar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel