Za mu fara sallaman masu cutar Korona daga asibiti ko da basu warke ba - NCDC

Za mu fara sallaman masu cutar Korona daga asibiti ko da basu warke ba - NCDC

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya wato NCDC ta sanar da cewa za'a fara sallaman masu cutar Coronavirus ko da gwaji bai nuna sun warke ba, sakamakon sabon binciken kimiyya da aka samu.

Binciken ya nuna cewa za'a iya sallamar masu cutar da suke fama da mura, zazzabi, ciwon jiki ko wasu alamu bayan akalla kwanaki goma suna jinya muddin alamun sun gushe, ko da gwaji bai nuna sun warke ba.

Amma masu cutar da basu fama da mura, zazzabi, ciwon jiki ko wasu alamu zasu yi kwanaki 14 a killace kuma za'a sallamesu ko da gwaji bai nuna sun barranta daga cutar ba.

Sun gina wannan shawara ne kan binciken da ya nuna cewa muddin cutar tayi kwanaki 14 a jikin mutum, ba zai iya shafawa wani ba.

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Za mu fara sallaman masu cutar Korona daga asibiti ko da basu warke ba - NCDC
Hoto: dakin killace masu Korona
Asali: UGC

Shugaban hukumar NCDC, Chikwe Ihekwazu, ya bayyana ranar Alhamis cewa: "Za mu daina jira har sai gwaji ya nuna cewa mutum ya warke daga cutar kafin mu sallameshi, kuma muna da tabbacin babu matsala, ba za ka iya shafawa yan'uwanka da abokai ba."

"Amma idan alamun cutar suka cigaba da bayyana a jikin mutum, zamu cigaba da kula da shi."

"Zamu fara sallaman wadanda alamun cutar ta bayyana a jikinsu cikin akalla kwanaki goma (10) ko goma sha uku (13) akasari, yayinda wadanda basu nuna alamu ba zamu sallamesu kwanaki 14 bayan gwajin farko da mukayi."

"Muna da tabbacin hakan ba zai kawo matsala ba, canji na da wuya."

Ihekwaezu ya kara da cewa duk wanda aka sallama sai ya koma gida ya killace kansa na karin mako daya kafin ya cigaba da rayuwa kamar yadda ya saba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel