Gwamnan jihar Katsina ya bude kasuwanni, ya umurci ma'aikata su koma bakin aiki

Gwamnan jihar Katsina ya bude kasuwanni, ya umurci ma'aikata su koma bakin aiki

- Gwamnatin jihar Katsina ta janye dokar hana fita

- An umurci ma'aikatan gwamnatin jihar su koma bakin aiki daga ranar Litinin

Gwamnatin jihar Katsina ta bude manyan kasuwanni 15 da aka rufe domin takaita yaduwar cutar Coronavirus kuma ta umurci ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki.

Manyan kasuwannin sun hada da na Charanchi, Mai'adua, Mashi, Dandume, Zango, Danja, Bakori, Yankara, Kafur, Dankama, Kaita, Kagadama, Dutsi, Garkin-Daura da Kayawa.

Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Alhamis.

Jawabin yace fari daga ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni, za'a bude kasuwanni, amma kada mutane suyi tunanin hakan na nufin cewa cutar Korona ta kare a jihar ne.

Hakazalika, gwamnatin jihar ta umurci dukkan ma'aikatan gwamnatin jihar da kananan hukumomi su koma bakin aikin fari daga ranar Litinin, 8 ga wannan watan.

KU KARANTA: Zulaihatu Nasir ta yiwa kishiyarta wanka da tafasasshen ruwan zafi a Kano

Gwamnan jihar Katsina ya bude kasuwanni, ya umurci ma'aikata su koma bakin aiki
Gwamnan jihar Katsina
Asali: Twitter

A wata sanarwa da sakataran din-din-din na ofishin shugaban ma'aikatan jihar, Lawal Ado Dutsinma, ya saki, ya yi bayanin cewa an sami izinin hakan bayan an janye dokan hana fita a jihar.

Sanarwar ta umurci dukkan sakatarorin ma'aikatu da shugabannin hukumomi su tabbatar da cewa ma'aikatansu sun bi sharrudan da aka gindaya domin komawa aiki.

Daga cikin sharrudan akwai bukatar samar da kayayyakin wanke hannu a dukkan ma'aikatu, wajibi ne ma'aikata su sanya takunkumin rufe baki kuma su rika baiwa juna tazara.

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel