Matasa sun hana tsohon soja ya kashe kansa a jihar Taraba

Matasa sun hana tsohon soja ya kashe kansa a jihar Taraba

Fiye da tsawon awa daya kenan, mazauna birnin Jalingo a jihar Taraba, sun yi ta kokarin kubutar da wani ma'aikacin soja daga yunkurin kashe kansa da tsakar rana.

Sojan mai suna Ali, ya hau ginin hasumiyar da ke kan iyakar shiga birnin Jalingo wanda aka yi wa tambari da 'lale maraba da zuwa Taraba' mai tsayin kafa 24, ya yi barazanar dirgowa.

Yana magana cikin harshen Hausa da gwamutsatsten Turanci ya na cewa, "Ina so na mutu. Ku bar ni kawai na dirgo na mutu.”

Amma Matasa sun yi cincirindo a wurin suna roƙonsa: “Don Allah kar ka dirgo. Ba ma son ka mutu."

An hango Ali a saman hasumiya mai tsayin gaske, yana kokarin dirgo wa, amma mutanen suna kokarin tabbatar da cewa sun ceci shi idan ya fado.

Ali yayin da Matasa ke kokarin kubutar da shi daga aika-aika
Ali yayin da Matasa ke kokarin kubutar da shi daga aika-aika
Asali: Twitter

KARANTA KUMA: Hoton wasu 'yan 6 da suka kammala karatun sakandire ya zagaya yanar gizo cikin sauri

Suna mai gargadi tare da kwantar masa da hankali da cewa, sun fi son ya canza tunaninsa kuma kada ya kuskura ya dirgo.

Shaidu sun ce halin da sojan ya jefa kansa ya janyo hankalin al'umma, yayin da aka hango shi a saman hasumiyar yana kwabe suturar da ke jikinsa kuma yana yin cilli da ita.

"Mun lura wani yana hawa hasumiyar kuma yana cire kayan sa. Isar mu wurin ke da wuya muka fahimci ashe wanda muka sani ne."

"Babu abinda ya rage face dan bante da kuma 'yar singileti a jikinsa, kuma yana yunkurin dirgo wa. Mun yi ta rokon sa a kan kada ya aika aikin da na sani," inji wani mai ba da shaida.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Gani na ido ya tabbatar da cewa, akwai rauni a kokon gwiwar kafarsa ta hagu, wanda take daure da bandeji.

Wata majiya ta shaidawa manema labarai na jaridar The Nation cewa, Ali yana fama da tabin hankali kuma ba dadewa aka sallame shi daga aiki.

"Tsohon soja ne, wanda ya saba yawo a kan baburan sojoji a cikin gari. An sallame shi daga aikin soja bayan ana gano yana da tabin hankali," inji wata majiyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel