Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 392 – DHQ

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 392 – DHQ

A kalla yan bindiga 392 ne suka bakunci lahira a yayin da Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da ‘Operation Accord’ a kan yan bindigan da ke tserewa daga yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya na kasar.

Jami'in watsa labarai na sojojin, Manjo Janar John Enenche ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa rundunar ta kaddamar da ‘Operation Accord’ ne domin cimma wannan manufar.

A cewarsa, "Dakarun rundunar na sama da kasa sunyi nasarar kashe yan bindiga 392 tun bayan kaddamar da atisayen a Katsina, hakan ya yi wa yan bindigan illa inda suka koma kai wa fararen hula hari.

"Babban hafson dakarun tsaro ne ya bayar da umurnin kaddamar da Operation ACCORD daga ranar 1 ga watan Yunin 2020”.

Sojojin Najeriya sun kashe yan bindiga 392 – DHQ
Sojojin Najeriya sun kashe yan bindiga 392 – DHQ. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya kara da cewa, "a yankin Arewa maso Gabas, Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro suna ragargazan yan taada musamman ta sama da kasa a karkashin atisayen Operation Lafiya Dole.

"Nasarorin da aka samu ya hada da kashe wasu manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP, lalata wuraren ajiyan makamansu da datse hanyoyin da suke amfani da su wurin safarar kaya.

"Yanzu duk a rikice suke saboda kashe manyan kwamandojinsu sakamakon hare haren sama da kasa da aka kai a mabuyarsu baya ga sumame da ake kai musu ta kasa.

"Yanzu karfinsu ya kusa karewa shi yasa suka koma mai hari a wuraren da suke zaton cin galaba amma duk da haka dakarun mu na Lafiya Dole suna fattatakarsu."

Enenche ya kara da cewa Operation ACCORD hadin gwiwa ne tsakanin rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro a kasar da aka kafa domin yaki da yan bindiga da sauran miyagu.

Ya yi kira ga alumma su cigaba da taimakawa rundunar da bayyanai masu amfani a kuma kan lokaci domin hakan zai taimakawa sojojin cimma manufarsu na samar da tsaro da zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel